--
Yadda Farashin Buhun Simintin BUA Zai Dawo A Yau Litinin 2 Ga Watan October

Yadda Farashin Buhun Simintin BUA Zai Dawo A Yau Litinin 2 Ga Watan October


A kokarin rage farashin Simintin da kuma nazari kan aiyukan mu da muka yi, a saboda haka Hukumar gudanarwar kanfanin Simintin BUA PlC na sanar da  dimbin abokan hudarmi cewar daga ranar *2* ga watan *Octoban 2023* mun yanke shawarar rage farashin Simintin. A saboda haka yanzu za'a rika sayar  Buhun Simintin BUA akan naira 3,500 Wanda hakan zai sa Yan Najeriya su ci gajiyar tsarin kafin kammala sabon  ginin sabbin kanfanonin Simintin mu.

Da zarar an kammala ginin sabbin kanfanonin Simintin, Wanda zai kara yawan Simintin da muke bugawa zuwa Tan milyan 17, a kowacce shekara, kanfanin Simintin BUA zai sake yin nazari kan farashin kamar yadda aka sanar a baya, a zangon farko na shekarar 2024.

*JAN HANKALI*  A kwana da sanin cewar duk wata tsohuwar oda  ko kayan Simintin da ba'a Kai ba, za'a  zabtare farashinsa zuwa naira dubu 3,500  akan kowanne Buhu, kamar yadda yake bisa sabon farashin da zai fara aiki daga  2 ga watan Octoban 2023.

Dillalanmu masu lasisi ana jan hankalinsu dasu tabbatar da cewar anyi aiki da wanann sabon farashin, a yayin da za'a sa ido domin tabbatar da bin doka da oda.

0 Response to "Yadda Farashin Buhun Simintin BUA Zai Dawo A Yau Litinin 2 Ga Watan October "

Post a Comment