--
Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Ba Dalibai Mata N20,000 Duk Wata

Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Ba Dalibai Mata N20,000 Duk Wata



Daga Auwal  Ahmed  Shaago

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta fara bayar da tallafin Naira 20,000 ga ɗalibai mata 45,000 domin tallafa wa ilimin ƴaƴa mata tare da ƙarfafa gwiwar iyaye su tura ƴaƴansu mata zuwa makaranta.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ƴancin kai wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

A kalamansa:

“Domin tallafa wa ilimin ƴaƴa mata da kuma kwadaitar da iyaye su tura ƴaƴansu mata zuwa makaranta, muna ba da tallafin Naira 20,000 ga yara mata sama da 45,000 a matsayin shirin gwaji don tallafa musu su ci gaba da karatu.”

“Har ila yau, muna shirin zamu sake kawo tsarin amfani da motocin bas domin jigilar yara mata zuwa makarantu da dawo da su.”

Abba Gida-Gida zai gina sabbin makarantu

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin sa tana kuma gina sabbin makarantu a fadin kananan hukumomi 44 a ƙoƙarin da suke yi na ganin sun kwashe duk yaran da ba su zuwa makaranta da ke yawo a kan tituna.

Hakazalika, ya nanata ƙudirinsa na tura dalibai 1001 da suka kammala karatun digiri na farko da daraja ta ɗaya zuwa ƙasashen waje domin yin digiri na biyu

0 Response to "Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Ba Dalibai Mata N20,000 Duk Wata"

Post a Comment