--
Fitaccen malamin Addinin musulunci na Najeriya Jagoran Yan Uwa Musulmi Sheikh  Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky Ya isa kasar  Iran

Fitaccen malamin Addinin musulunci na Najeriya Jagoran Yan Uwa Musulmi Sheikh Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky Ya isa kasar Iran


Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Yaqoub AL-ZAKZAKY ya isa kasar Iran a wani bangare na ziyararsa ta biyu zuwa kasashen waje bayan da samun nasararsa a kotu  tare da kuma  sakar masa fasfosdinsa.

 A ranar Laraba ne Shaikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim suka isa filin jirgin saman Imam Khumaini da ke babban birnin kasar Iran wato birnin  Tehran, inda al'ummar kasar Iran da Tare da Dalibansa suka tarbe su bayan isowarsu.

 Mahalarta taron a cikin daruruwansu sun rike alluna tare da daga tutocin kasar Iran da kuma hotunan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da marigayi kwamandan yaki da ta'addanci Laftanar Janar Qassem Soleimani domin nuna goyon baya ga fitaccen malamin addinin Musuluncin na Najeriya.

 "Na yi matukar farin ciki da irin wannan taron jama'a na goyon bayan juriya a yau, kuma ba abin da zan ce sai godiya ga masoya," in ji Shaikh Zakzaky a wani jawabi da ya yi a filin jirgin sama.

 Da yake ishara da alkawalin da Allah ya yi na cin nasarar gaskiya a kan karya, ya ce: “Dukkanmu muna cikin jarrabawa mai girma, kuma ana fatan juyin juya halin Musulunci ya kawo sauyi a duniya baki daya, ciki har da Amurka da Turai.  ya kafa tushen fitowar limamin  Zamaninmu na karshe, Imam Mahdi (A.S).”


Credit:Abubakar Abdullahi Yusuf 

0 Response to "Fitaccen malamin Addinin musulunci na Najeriya Jagoran Yan Uwa Musulmi Sheikh Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky Ya isa kasar Iran"

Post a Comment