Wasu daga cikin matsaloli, a matakai daban-daban na rayuwa
Matsaloli a matakin Matasa;
Daga Aisha Kazimiyyah
Wasu matasan na fama da rashin ingantattun abin koyi a gida, a makaranta da kuma cikin al’umma, domin ba su ga mutanen da suka dace ba, a duk rayuwarsu. Wasu matasan suna samun kansu a cikin gungun jama’a mashaya miyagun kwayoyi a titi, barasa, halayen banza, tashin hankali, da laifuffukan da suka zama ruwan dare, kuma suna shiga cikin waɗannan abubuwa masu halakarwa.
Wasu matasan a rayuwarsu ba su taɓa samun wanda zai sanar da su mahaliccin su ba, ba su taba shiga wata rayuwa da suka ji cewa su waye ne ya kamata su san manufar hakittar su, haka kawai suke rayuwa kara zube. Haka kuma wasu matasan ana hana su karatu, domin suna rayuwa a wajen da karatu ba shi da muhimmanci.
Wasu matasan sun sami kansu a cikin yanayi na rugujewar gidajen mahaifansu, don haka yasa suka kasa samun rayuwa ta yau da kullun mai kyau. Wasu kam ma sun zama marayu, tun kafin su san kansu. Wasu matasa suna tashi ba kula bare kwaɓa, yanayi ma yasa suka nesanci iyayen su.
Wasu matasan suna rayuwa cikin tsoro, kuma sun tsinci kan su a gudun hijira saboda yaƙe-yaƙe, da rikice-rikice. Wasu matasan suna fama da rashi, wasu kuma suna fama da cin zarafi na halittar su, ta jiki ko ta hanyar samar da su zuwa wannan duniyar.
Wasu matasan a rayuwar su ba su taɓa ganin dangantakar iyali da ta dace ko kuma rayuwar iyali ta dace ba, sun rayu ne a inda ba'a ganin kimar dangatar iyali. Wasu matasan suna fama da tabin hankali, wasu kuma suna fama da naƙasasshen karatu.
Wasu matasa suna fama da talauci da rashi iri-iri. Wasu matasa suna aiki a cikin mawuyacin yanayi, kuma a hana su neman ilimi. Wasu matasan ba sa iya magana, karantawa da rubutu a kowane harshe.
Wasu samari an hana su ƙauna, an ƙyamace su, ba'a ba su kulawa ba. Wasu matasan an hana su ƴancin su na buƙatun ɗan adam. Wasu matasan a titi suke kwana. Wasu matasan sun zama mashaya, masu shan muggan kwayoyi a titi, ƴan daba a tituna, ƴan caca, rashin son zaman lafiya ga jama’a, masu laifi, wanda ake lalata da su, da sauransu.
Ire-iren Waɗannan matsalolin suna daga cikin matsalolin da wasu matasa ke fuskanta. Ta yaya ba za a samu matsala ba? Yaya za a yi a magance wannan matsalar?
0 Response to "Wasu daga cikin matsaloli, a matakai daban-daban na rayuwa"
Post a Comment