--
Kakakin gwamnatin sojan kasar Nijar Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce sun dakile guduwar bazaun

Kakakin gwamnatin sojan kasar Nijar Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce sun dakile guduwar bazaun


Gwamnatin mulkin sojan kasar Nijar ta ce ta daƙile wani yumƙurin hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum na tserewa tare da iyalinsa a ranar Alhamis.

Ana tsare da Bazoum da matarsa da kuma ɗansa ne tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatinsa a cikin watan Yuli.

Kakakin gwamnatin sojin Nijar, Kanar-Manjo Amadou Abdramane, wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya yiwa jama’ar ƙasar ta Talabijin ya ce Bazoum da iyalinsa sun tsara guduwa daga fadar shugaban ƙasar ne da misalin ƙarfe uku na dare.

Ya ce hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ya yi kokarin tserewa da karfe 3 na safiyar ranar Alhamis tare da iyalansa masu dafa masu Abinci 2 da kuma jami’an tsaro guda 2.


Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce ‘’matakin farko na wannan shiri shine na su fice daga cikin fadar zuwa kewayen wurin inda wata mota ke jiransu daga nan ne za a dauke su zuwa wani gida da ke cikin unguwar Tchangarey a , daga nan kuma a nufi wani wuri inda wasu jirage biyu masu saukar ungulu na wata kasa da sanarwar ba ta bayyana ba za su kai su Birnin Kebbi da ke tarrayar Nijeriya’’

Sanarwar sojojin ta kuma jinjinawa sojojin da hazakarsu da kuma hiimar su ta ba da damar dakile wannan yunkurin tare da kare rayuka.

Shugaba Mohamed Bazoum dai ya kasance tsare tun bayan da jami'an tsaron fadarsa suka kifar da gwamnatinsa suke kuma cigaba da yin garkuwa da shi tun karshen watan Yuli.

Lamarin ya yi sanadiyyar raba gari tsakanin kasar ta Nijar da uwargijiyarta Faransa ta hanyar korar jakadanta da kuma sojojinta 1500 da ke yaki da kungiyoyin masu da’awar jihadi a yankin Sahel musaman a yankin iyakoki 3.

Nijar dai na daya daga cikin kawayen kasashen yammacin duniya a yankin Sahel da suke yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai masu alaka da Al-Qaeda da IS.

A kan haka ne kungiyoyin yammacin Afrika irin su ECOWAS da UEMOA suka kakabawa kasar takunkumi domin tillastawa sojojin mayar da hanmabararen shugaban kasar Mohamed Bazoum.

0 Response to "Kakakin gwamnatin sojan kasar Nijar Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce sun dakile guduwar bazaun "

Post a Comment