--
DAGA NASIRU SALISU ZANGO FITACCEN DAN JARIDA

DAGA NASIRU SALISU ZANGO FITACCEN DAN JARIDA

Yansanda na halin tsaka mai wuya…
Ina jajantawa iyalan marigayi player da wani dansanda ya harbe shi kuma Ina jinjinawa kwamishinan yansandan jihar Kano bisa matakin gaggawa da ya dauka na umarnin kama dansandan da yayi harbin.
Amma Mu sani matukar Muna son ganin bayan daba a Kano tilas Mu baiwa yansanda hadin Kai domin Sannu a hankali matsalar kullum kara ta‘zzara take.

Da yawan yan dabar fa a lokuta da dama yunkuri suke suyi gaba da gaba da yansanda kaga suna yunkurin afka musu,a Irin wannan yanayi ne yansanda ke tsintar Kan su a yanayin tsaka mai wuya.
Nasan daga shaidar da ake bayarwa marigayi player Ba dan daba bane illa tsautsayi da ya hau Kan sa a dalilin yandabar unguwar su ko kuma kusa da unguwar su,Ashe Kenan ko Mu Ba yandaba bane ayyukan yan dabar zai iya jawo mana masifar da Zata gama damu.
Yan daba a yanzu sun yi karfi suna iya afkawa yansanda da makamai domin sun Ba koyaushe zasu iya harbin su ba .


A kwanakin baya a gaba na wani dan daba yayi yunkurin cakawa dansanda wuka duk da bindigar dake hannun dansandan,da kyar Allah ya kwace shi watakila kuma dansandan yaki yin harbi ne gudun kada yazo ana maganar yayi harbi ba bisa ka‘ida ba, a saboda haka nake ganin ya zama wajibi Mu zauna a unguwanni Mu bullo da hanyar hada Kai da yansanda domin dakile daba wacce gashi Tana jawo mana asarar rayukan mutanen kirki Irin su player Wanda yawancin mutanen yankin su ke bada shaidar cewa mutumin kirki ne , Allah ya gafarta masa amma a gaskiya yansanda na cikin halin tsaka mai wuya musamman wajen yaki da yandaba.
Allah ya kawo nan akarshen matsalolin Mu amin.

0 Response to "DAGA NASIRU SALISU ZANGO FITACCEN DAN JARIDA"

Post a Comment