--
KISAN MUSULMAI A KADUNA: Ba Kawai Magana Za'a Yi Ba Wajibi Ne A Ɗauki Matakin Kisan Da Aka Yi A Kaduna

KISAN MUSULMAI A KADUNA: Ba Kawai Magana Za'a Yi Ba Wajibi Ne A Ɗauki Matakin Kisan Da Aka Yi A Kaduna


Daga Idris  Jos 

   Cewar Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos 

Muna masu miƙa sakon ta'aziyya ga ƴan'uwa musulmai da aka kashe su a bisa zalunci, a yayin da suke taro muhimmi taron mauludin Manzon Allah Muhammad Rasulullah (Saww). Wanda ya tabbata cewa sojojin Nigeriya suka yi wannan aika-aika, wannan babban abin bakin ciki ne , babban abin da ya kamata al'ummar musulmi maza da mata manya da ƙanana musamman malamai da wanda suke da iko na al'umma a akan su da su fito suyi magana , ba kawai magana ba a ɗauki mataki.

Lokacin da aka kashe wannan bayin Allah ba wanda yayi magana, har ma wasu kafafen labarai sun ƙaryata , sai daga baya sojojin da kansu suka yarda cewa su suka yi amma bisa kuskure. In sun ce a bisa kuskure ne , abin da muke so Lallai haƙƙi ne a biya diyyar wannan bayin Allah da aka kashe su mazan su da matan su yadda Addinin Musulunci ta tanadar.

Wajibin Sojojin Najeriya dama gwamnatin Nijeriya ta fito ta nemi afuwan ƴan uwa wannan mutane, a basu hakuri, akai musu ɗauki, sannan a biya diyyar rayukan su da abubuwan da aka hallakar, in an yi haka sai muce anyi abin da ya dace. Amma idan ba'a yi haka ba wannan ya tabbata zalunci ne ƙarara . Kamar yadda Israel take kashe maza da mata da jarirai a Gaza da Palestinu sai muce wannan abin yayi kama da haka.

Daman an taɓa yin irin wannan , an kashe ƴan uwa musulmi almajiran maulana Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), har ma sojojin Nigeriya sun binne mutane da rayukansu kamar yadda ya tabbata ba tare da yi musu sutura na Musulunci ba. Har yau ɗin nan basu fito sun nemi afuwa ba, ballantana a nemi diyya wannan babban zalunci ne ƙarara. Kafin wannan ma mun ga abin da aka yiwa mahaddata Alkur'ani, can ma gwamnati bata yi komai a kai ba.

Wannan abin da ya faru a Kaduna har yanzu shugaban ƙasa bai yi magana ba, babu wanda yayi magana daga cikin jami'an gwamnati, sai daga baya muke jin wai Gwamna Kaduna ya naɗa kwamiti bincike abin da ya faru. To, ba kawai a yaudari mutane da sunan kafa Kwamiti bane muji shiru kamar an raka bawa garin su. Abin da muke so shine gwamanti ta je wannan gari a jajantawa wannan bayin Allah a nemi afuwan su a biya su diyya, kuma wanda suka yi wannan abin a hukunta su. 

Al'ummar nan da aka kashe ba sun je daji bane taron mauludi a cikin garin su aka same su, kuma kowa ya sani a garuruwa birni da kauye ana tarukan mauludin Manzon Allah (Saww), ba a gansu da bama-bamai ba aka jefa musu Bom ace wai kuskure ne, wannan ta tabbata irin abin da yahudawa Isra'ila take yiwa Gaza ne suke aikawa tawa a wannan ƙasa ta wani fuska.

Babban abin damuwa shine Musulmi basu farka ba, nau'i ne na makirci na faɗa da addini wanda ya kamata musamman malamai suyi faɗa da wannan abin da babban murya cewa dole a biya diyya wannan abin. Ba ana maganar cewa ɗan ƙungiyar ku ne ko ba ɗan ƙungiyar ku bane, an taɓa musulunci ne. Idan kana tunanin ba ɗan mazhabar ku bane to gobe Wannan al'amari zasu iya faɗo dashi akan ku.

Kamar yadda suka yi a kan masu mauludi haka suka yi akan almajiran maulana Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), suka zo da muggan makamai suka yi kisa na wulaƙanci da makamai da ba'a taba ganin irin su ba. Ciki wanda aka kashe harda ƴaƴan Sayyid Zakzaky (H) guda uku shima da matarsa ba'a bar su ba , musulmai suka yi shiru a wancan lokacin gashi yanzu sun kara canza salo suna kai hari cikin al'ummar musulmi ba ƴan shia kaɗai ba ake kashewa.

Dole musulmai mu tashi daga baccin da muke, mu sani duk abin da ya taba musulmi ya taba mune duka, wannan zalunci da abin da yake gudana a Duniya mus sani sabon salo ne na ƙarar da musulmi da musulunci a duniya, idan kunne yaji gangan jiki ya tsira.

   

0 Response to "KISAN MUSULMAI A KADUNA: Ba Kawai Magana Za'a Yi Ba Wajibi Ne A Ɗauki Matakin Kisan Da Aka Yi A Kaduna"

Post a Comment