--
Kungiyar kiristoci ta Yankin Arewa Sun  yi kira ga Shugaban kasa Ahmad  Tinubu da ya tsawatar wa alkalan Kotun Daukaka Ƙara kan hukuncin zaben shekarar 2023

Kungiyar kiristoci ta Yankin Arewa Sun yi kira ga Shugaban kasa Ahmad Tinubu da ya tsawatar wa alkalan Kotun Daukaka Ƙara kan hukuncin zaben shekarar 2023



Kungiyar Fastoci Kiristoci Yan  asalin  Yankin Arewa, ACIPA, ta yi  kira ga shugaban kasar Nageria Ahmad Bola Tinubu da ya tsawatar wa  Da alkalan Kotun Daukaka karar kasarnan kan irin yanke hukuncin da su ka yi akwanakin nan akan zabukan da aka yi a wasu sassa na ƙasar nan, innda suka siffanta shi da “rashin adalci ƙarara.

Shugaban kungiyar, Rabaran Luke Shehu ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya fitar  a ranar  Lahadi a garin Jos.

Ya ce hukuncin ya zama “abin kunya a kasa”.

Shehu ya bayyana cewa hukunce-hukuncen da kotun daukaka kara ta yanke a baya-bayan nan da ta kori wasu ‘yan majalisar tarayya daga jihar Filato “zalunci ne”.

Ya nace cewa dole ne shugaban kasa ya shiga tsakani domin dawo da amincewar jama’a ga bangaren shari’a “da dimokuradiyya gaba daya”.

“Muna so mu yi amfani da wannan Dama wajen yin kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya tsawatar wa Alkalan Kotun Daukaka Karar suna bukatar a tuna cewa har yanzu bangaren shari’a shine fata na karshe ga talaka.

“Muna kuma so mu tunatar da shugaban mu cewa kasashen duniya suna kallo yayin da bangaren shari’a ke yin furuci da ke nuna cewa an fara fitar da rai daga tsarin adalci da dimokuradiyya.

0 Response to "Kungiyar kiristoci ta Yankin Arewa Sun yi kira ga Shugaban kasa Ahmad Tinubu da ya tsawatar wa alkalan Kotun Daukaka Ƙara kan hukuncin zaben shekarar 2023"

Post a Comment