--
Tirkashi! Jihar Katsina ce ta 4 cikin jirin jihohin da suka fi yawan masu cika aikin kuratan ƴan sanda a shekarar2023 , inda sama da mutum 30,000 suka cike daga nan jihar Katsina

Tirkashi! Jihar Katsina ce ta 4 cikin jirin jihohin da suka fi yawan masu cika aikin kuratan ƴan sanda a shekarar2023 , inda sama da mutum 30,000 suka cike daga nan jihar Katsina


Yayin da jihar Katsina ta shiga gaban yawan Kano wajen masu neman aikin kuratan yan sandan, sai dai jihar Kaduna ce ta zo ta ɗaya baki ɗaya

Ƙasa da sati ɗaya a kulle manhajar daukar sabbin kuratan yan sanda a Nijeriya, amma kawo yanzun, sama da mutum dubu dari biyar da arba'in da bakwai e, da dari bakwai da saba'in da hudu (547,774) ne suka ciki

Daga cikinsu, jihar Kaduna ce ta zo na ɗaya a wajen yawan masu neman wannan aikin, inda mutum 40,262 yan asalin jihar suka cike neman aikin a intanet, yayin da jihar Adamawa ta zo na biyu a yawan masu neman aikin har mutum 36,398, sai jihar Borno ta zo ta uku da yawan masu neman aikin 31,122.

Haka kuma jihar Katsina ce ta zo ta hudu a cikin wadanda suka cike neman aikin kuratan yan sandan inda mutum 30,604 yan asalin jihar suka nema, sai jihar Kano ta zo ta 5 da yawan masu neman aikin 30,004

Wani abin mamaki jihohin Kudu, sune jihohin da suka fi koma baya, na yawan matasan da suka cike neman aikin daga jihohinsu, inda jihar Anamnra ta zo jiha ta karshe ga wadanda ba su nemi aikin sosai ba, da ke da mutum 1664 kadai, sai kuma jihar Ebonyi mai mutum 2132 kacal, yayin da Legas ita ce jiha ta ukun karshe mai mutum 2324.

Haka kuma hukumar ta bayyana wancakalar da mutum 190,741 tun a wannan lokacin da ba a je ko'ina ba, domin saba wa dokokin cike aikin.

Za a iya tuna cewa Katsina Daily News ta rawaito mak cewa, hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana bude manhajar masu sha'awar shiga aikin kuratan yan sandan Najeriya, a intanet tun daga ranar  15 ga watan Oktoba 2023, har zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba 2023 da za ta kulle manhajar.

Duk da a wannan sanarwar hukumar ba ta bayyana adadin yawan kuratan yan sandan da za ta dauka ba a wannan shekarar, amma tun bayan hawan tsohon shugaban kasa Buhari, a kudan duk shekara hukumar ba ta wuce daukar sabbin kuratan yan sanda dubu goma (10,000) a duk fadin Nijeriya.

Credit: Katsina Daily News. 

0 Response to "Tirkashi! Jihar Katsina ce ta 4 cikin jirin jihohin da suka fi yawan masu cika aikin kuratan ƴan sanda a shekarar2023 , inda sama da mutum 30,000 suka cike daga nan jihar Katsina"

Post a Comment