Labari Mai Dadi Ga wandanda suka Cike NDE: Yadda Zaku Duba Abinda Kuka Cike yayi daidai a Shirin Samar da Ayyuka 93,731 na Hukumar NDE Duba Cikakken Bayani
A karkashin Tsarin "Renewed Hope Agenda" na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da rage talauci, Hukumar Samar da Ayyukan Yi (NDE) ta kaddamar da shirin koyar da sana'oi da ake cikewa daga watan Oktoba zuwa Disamba 2024.
Wannan shirin ya kunshi horar da mutane kan sana'o'i guda 30 don rage matsalar rashin aikin yi da karfafa samar da arziki a Najeriya.
Domin tabbatar da cewa shirin ya samu tasiri ga jama'a a matakin kasa, ana aiwatar da shi ne a matakin mazabar zabe.
Sanarwa ga masu neman shiga shirin:
Wa'adin neman shiga shirin "Creation of 93,731 Jobs Initiative" ya riga ya wuce.
Ana shawartar masu neman shiga su shiga shafukan su na yanar gizo don:
- Duba matsayin neman aikin su.
- Saukar da bayanan neman aikin da suka gabatar.
Yadda Zaku Duba Aikace-aikacenku:
Shiga shafin yanar gizon NDE: https://nderegistrationportal.ng/
Shigar da Email da Password din ku sannan ku latsa Login.
Bayan kun shiga, latsa View Programme Details A nan, za ku ga zabi mai suna Download Application Data; ku latsa don saukar da bayanan aikace-aikacenku.
Source: Haske News
0 Response to "Labari Mai Dadi Ga wandanda suka Cike NDE: Yadda Zaku Duba Abinda Kuka Cike yayi daidai a Shirin Samar da Ayyuka 93,731 na Hukumar NDE Duba Cikakken Bayani"
Post a Comment