
Babbar Dama ga Daliban Nigeria: NNPC / TotalEnergies National Merit Scholarship Scheme 2024/2025 – An Buɗe Rajista!
NNPC / TotalEnergies National Merit Scholarship Scheme 2024/2025 – An Buɗe Rajista
TotalEnergies Upstream Nigeria Ltd. (TUPNI) tare da hadin gwiwar NNPC sun buɗe damar neman tallafin karatu na kasa ga ɗaliban jami’a a Najeriya. Wannan tallafi yana da nufin taimakawa ɗalibai wajen biya da rage nauyin kuɗin karatu.
Abinda Tallafin Yake Ciki:
- Ana bayar da shi ne ga daliban 100 da 200 level na cikakken karatun digiri a kowane fanni.
- Ana biyan tallafin daga shekarar da aka ci zuwa ƙarshen karatun.
- Taimako ne na shekara-shekara don rage nauyin kuɗin makaranta.
Sharuddan Cancanta:
- Dole ne mai nema ya kasance dalibi na cikakken lokaci a jami’ar da NUC ta amince da ita.
- Dole ne ya kasance a 100 ko 200 level a lokacin nema.
Wanda Baya Cancanta:
- Daliban da suka fi 200 level
- Daliban 200 level da CGPA ya kasa 2.5 (a tsarin 5.0)
- Wadanda suka taɓa karɓar wani tallafin makamanci daga kamfanonin mai
Yadda Ake Nema:
- Ana cike fom ne kawai ta yanar gizo:
- Kada a aika da kowanne application ta wasiƙa.
- Rufewar nema: Talata, 1 ga Yuli, 2025*
Bayanan Ƙari:- Za a gayyaci 'yan takara da aka zaɓa kawai zuwa jarrabawar tantancewa.
- Ƴan takara su tanadi kuɗin tafiya zuwa cibiyar jarrabawa mafi kusa da su. Latsa NAN Domin Apply Cikewa
📌 Ka tabbata ka cika kafin ranar ƙarshe domin kada ka rasa wannan babbar dama!
0 Response to "Babbar Dama ga Daliban Nigeria: NNPC / TotalEnergies National Merit Scholarship Scheme 2024/2025 – An Buɗe Rajista!"
Post a Comment