--
Sunayen Wadanda Suka Samu Shiga Shirin SUPA ITF Daga Jihohi 36 da FCT Sun Fito – Duba Sunanka Yanzu

Sunayen Wadanda Suka Samu Shiga Shirin SUPA ITF Daga Jihohi 36 da FCT Sun Fito – Duba Sunanka Yanzu

Sunayen Wadanda Suka Samu Shiga Shirin SUPA ITF Daga Jihohi 36 da FCT Sun Fito – Duba Sunanka Yanzu!

Hukumar Industrial Training Fund (ITF) ta fitar da sunayen wadanda suka samu shiga cikin shirin SUPA ITF daga kowace jiha a Najeriya, har da Babban Birnin Tarayya (FCT).

Shirin SUPA ITF wani shiri ne da ke bai wa matasa damar samun horo da ƙwarewa a sana’o’i da fasahohin zamani, domin ƙarfafa tattalin arzikin gida da rage zaman banza.

Yadda Zaka Duba Sunanka

Idan ka nemi shiga shirin a baya, to ga yadda zaka duba jerin sunayen:

1. Danna link ɗin da ke cikin comment ko post. 

2. Ka yi scroll ƙasa har ka ga jerin sunayen jihohi. Zaka ganshi kamar haka 

3. Zaɓi jiharka daga jerin. 

4. Sauke fayil ɗin PDF domin duba sunanka cikin sauƙi.

Jerin ya ƙunshi dukkan jihohi 36 da kuma FCT Abuja, don haka kowa na da damar dubawa cikin sauƙi.

Taya Murna!

Muna taya duk wadanda suka samu shiga shirin murna, tare da fatan za su ci gaba da amfani da damar don inganta rayuwarsu da al’umma baki ɗaya.

2 Responses to "Sunayen Wadanda Suka Samu Shiga Shirin SUPA ITF Daga Jihohi 36 da FCT Sun Fito – Duba Sunanka Yanzu"