--
Babbar magana: Nan gaba kadan maza za su rasa matan da za su aura Duba dalilai >>>

Babbar magana: Nan gaba kadan maza za su rasa matan da za su aura Duba dalilai >>>


Wani bincike kan alkaluman jinsi a duniya ya gano cewa wasu matakai da mutane ke dauka a kan haihuwa za su kawo karancin mata a duniya a nan gaba. 


Rahoton binciken da cibiyar lafiya ta BMJ Global Health ta gudanar kan bambanci tsakanin jinshi, ya nuna son haihuwar ’ya’ya maza da kuma al’adar kyamar haihuwar mata sun sa ana yawan zubar da cikin ’ya’ya mata ko kashe jarirai mata a wasu kasashe.


Binciken da cibiyar ta gudanar a wasu kasashe 204 ya nuna daga shekarar 1979 zuwa 2017 an kashe jarirai mata ko an zubar da cikinsu sau miliyan 45, in ji Aminiya. 


Sakamakon binciken ya ce a shekarar 1970 da ’yan kai, jararai maza da aka haifa a Kudancin Turai da Asiya sun fi mata, kasashen Indiya da Pakistan kuma ke da kashi na 95 cikin 100 na jarirai mata da aka zubar da cikinsu ko ake kashewa. 


Marbucin rahoton, Dokta Fengqing Chao, ya ce a halin yanzu, maza na fama da karancin matan da za su aura a wasu daga cikin kasashen da abin ya shafa. 


Rahoton ya ce Najeriya da Pakistan na daga cikin kasashen da nan gaba maza za su iya fin mata yawa, amma abin zai yi sauki bayan shekara 20 masu zuwa. 


Dokta Chao ya ce daga yanzu zuwa shekarar 2030 akwai yiwuwar rasa jarirai mata 4.7 kuma illar ta wuce batun rashin samun matar aure. 


Ya ci gaba da cewa idan ba a yi wa tufkar hanci ba, nan gaba a cikin ko wadanne maza uku, mutum daya ne zai samu matar da zai aura. 


Don haka, a cewar rahoton: “Akwai bukatar yin dokoki da za su tabbatar da daidaiton jinsi domin magance karancin abokan arue. “Karancin mata a cikin al’umma na iya haifar da miyagun dabi’u da tashin hankali da kuma kawo cikas a zamantakewar al’umma.” 


Muna matuƙar buƙatar mazajen aure, ƴan matan Gombe sun koka A wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo, wasu mata marasa aure a jihar Gombe sun yi kukan neman taimako kan rashin samun mazajen aure. 


Jaridar The Nation ta rahoto cewa mummunan lamarin ya ci gaba tsawon wasu shekaru a yankin arewa maso yammacin kasar, inda ta kara da cewa daruruwan mata marasa aure karkashin jagorancin Suwaiba Isa sun mamaye jihar Zamfara. 


Sun yi hakan ne don zanga-zangar rashin samun mazajen aure ga kimanin su 8,000 a watan Satumban 2018. Legit.ng ta tattaro cewa sarkin Yarbawa a Gombe, Abdulrahim Alao Yusuf, ya ce kashi 60% na mutanen da ba ‘yan asalin jihar bane sun fito ne daga yankin kudu maso yammacin kasar. 


Daya daga cikin mazauna jihar Gombe, Godiya Adamu, ta ce shekarunta 35, har yanzu ba ta samu miji ba, tana mai dora alhakin halin da ake ciki kan rashin samun namijin da ke son aure da gaske. Ta bayyana cewa ta yi soyayya na kimanin shekaru biyar ba tare da sakamako mai ma'ana ba kafin daga baya ta hakura. 


Ta ce: “Me zan yi? Ba zan iya cusa kaina ga maza ba idan ba su zo ba. A iya sani na, rayuwa na ci gaba da miji ko babu miji." Wata Bafulatana, mai suna Amina, ta ce matsalarta ita ce ta yi karatu, tana mai cewa ta gano cewa yawancin maza a arewa ba sa son auren mata masu ilimi. Amina ta lura: 


“Wataƙila saboda suna ganin ba abu mai sauƙi ba ne a gare su su juya irin wannan matar son ransu. Don haka a wurina, zaɓin shi ne na ci gaba da zama ba aure sannan na zamo uwa da uba ga yarana.” 


Source: Legit

0 Response to "Babbar magana: Nan gaba kadan maza za su rasa matan da za su aura Duba dalilai >>>"

Post a Comment