--
Yanzu yanzu: Kalli hoton yadda 'Yan kungiyar Biyafara suka kone mota guda cike da mutane

Yanzu yanzu: Kalli hoton yadda 'Yan kungiyar Biyafara suka kone mota guda cike da mutane


 Daga Auwal Albarno


A wani saka dokar hana fita na duk ranar litinin da Kungiya masu fafatikar kafa kasar Biyafra da ta kudu maso gabashin Nigeria, saboda nuna goyon bayan su na rashin jindadin kama masu shugaban tafiyar Mazi Nmadi Kanu. 


Wannan dokar ta sa ko wanne shago rufewa a yankunan tasu da suka hada da Engugu, Imo, Anambara da sauran su. 


Lamarin na yau wanda labari da wasu jaridu suka yada, na nuna cewa an kona motoci dauke da pasinja, Wanda hakan na iya zama akwai 'yan arewa cikin su wayan da aka kona.


Wannan lamarin na kara nuna cewa Kasar Biyafra akwai matsala, wanda ba iya Yan arewa kawai ba, kusan kowa ma na fuskantar barazana sakamakon wannan abubuwa da ke faruwa.


Hatta wasu Yan kabilar Igbo din ma wannan lamarin ya shafe su.


Biyafra na da yancin yin abinda suka ga dama na shirin Daawar ballewa, ko zanga zanga, ko nuna jimamin kame shugaban su. Amman basu da ikon kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba. Domin hakan laifi ne, Allah ba zai yafe musu ba.


Matukar kungiyar zasu ci gaba da irin wannan to zasu iya fadawa gagarumar matsala da zai sa zasuyi biyu babu a tafiyar su.


Babu wanda zai goya musu baya idan har suka ci gaba da kashe mutanen da ba ruwan su.


Allah ka jikan wayan da suka rasu, kasa Aljanna ce makomar su.


#Ameen

#Press2021

0 Response to "Yanzu yanzu: Kalli hoton yadda 'Yan kungiyar Biyafara suka kone mota guda cike da mutane"

Post a Comment