--
Kada ku auri duk namijin da yake da wannan dabi'ar – Budurwa ta shawarci ‘yan mata duba abinda tace

Kada ku auri duk namijin da yake da wannan dabi'ar – Budurwa ta shawarci ‘yan mata duba abinda tace


Wata kyakyawar budurwa mai ban dariya ta bawa ‘yan mata shawarar da ta jawo akayi ta tafka muhawara a kafofin sadarwa na zamani.


A wani rubutu da ta wallafa a shafin ta na twitter, ta baiwa ‘yan mata shawarar da suyi watsi da maganar auren duk wani namiji mai wanka sau uku a rana.


Sai dai kuma wani abin mamaki, shine, jami’ar Harvard ta fannin likitanci dake kasar Amurka ta taba wallafa wani rubutu wanda yake kama da abinda budurwar ta, hakan ya sanya wasu ke ganin abinda budurwar ta fada gaskiya ne.


Budurwar ‘yar asalin kasar Ghana dake zaune a Najeriya ta jawo kace nace a kafar sadarwa ta Twitter, bayan ta samu da dama sun ba ta goyon baya kan wannan magana da tayi.

fata

Ma’abociyar rubutun barkwancin mai suna @heiressjacinta ta baiwa yan uwanta mata shawara akan namijin da yakamata karsu saurara a yayin maganar aure, inda ta ce:

Idan yana wanka sau uku a rana, karki aureshi mazan gaske basa son wanka

A cewar rubutun da jami’ar Havard ta fitar ta ce:

Yawan yin wanka a rana yana iya zama illa ga lafiyar mutum.

Wasu dalilan da aka bayar


Wanka akai-akai zai iya haifar da bushashiyar fata wacca zata iya barin kwayoyin cuta da kuma lalacewar garkuwar jiki wanda yake iya kawo lalacewar fata


Sannan, sabulai masu dauke da sinadarin yaki da kwayoyin cuta a cewar rubutun suna kashe kwayoyin cuta, saboda haka suna rikita kananan kwayoyin hallitar da da suke kan fata kuma zata karfafa karuwar wasu cuttukan na daban, juriya ga maganin rigakafi.


Daga karshe, tsarin rigakafin jiki yana bukatar adadin kara kuzari daga kananun hallitu da kuma datti saboda samun garkuwar jiki.


Ta kawo wadannan dalilan ne har zuciyarta ko kuma yana daya daga cikin barkwancin ta.


@heiressjacinta

Ra’ayoyin mutane

“Kazaman mata suna wanka sau daya, ya labarin su su kuma??”


@ThursdayBone

“Ina wanka sau biyu a rana, inaga nayi daidai.”


@mcboom100

“Mungode da kika kawo maudu’i mai ma’ana.”


@Trega_Edem

0 Response to "Kada ku auri duk namijin da yake da wannan dabi'ar – Budurwa ta shawarci ‘yan mata duba abinda tace"

Post a Comment