--
Kalli zafafan Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma

Kalli zafafan Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma


An fara gudanar da shagalin bikin mika wa Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma.


Bikin na gudana ne a yau Asabar, 21 ga watan Agusta a masarautar Bichi Tuni manyan baki irinsu, Sarkin Musulmi, Sarkin Kano da Shehun Borno suka isa wajen taro


Surukin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, zai amshi sandar girma a yau Asabar, 21 ga watan Agusta. 


Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan daura auren ‘yarsa, Zahra Bayero da dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari. 


Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa tuni aka fara bikin wanda ke gudana a Masarautar Bichi da ke Jihar Kano. 


Zuwa yanzu daga cikin manyan baki da suka hallara a wajen akwai Sultan na Sokoto kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III. 


Har ila yau, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda yakasance ɗan uwan sarkin na Bichi ya hallara a wajen bikin bayan rashin halartar ɗaurin Zarah da kuma Yusuf a ranar Juma'a, 20 ga watan Agusta. 


Hakazalika mai alfarma Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai ya hallara a wajen taron. 


Sauran sune Sarakunan Zazzau, Amb Ahmed Nuhu Bamali, na Daura Umar Farouk Umar, Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Lafiya, da mataimakin gwamnan Zamfara, da sauran su, Daily Trust ta ruwaito. 


An tsaurara matakan tsaro tun daga mashigar garin tare da jami'an tsaro daban -daban da ke kokarin tabbatar da doka da oda. 


Kalli Hotuna Aqasa: 


Source: Legit

0 Response to "Kalli zafafan Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma "

Post a Comment