Kasurgumin mai fashi da makami da 'yan sanda suka kama a Kano yayi Jawabi Cikin wannan Bidiyon >>>
Jami'an yansandan jihar Kano sun kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Mohammed Ibrahim bayan ya aikata fashi da makami.
Kakakin hukumar yansandan jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa manema labarai.
Ya ce an kama.dan fashin ne ranar 16 ga watan Agusta bayan ya aikata fashi da makami. Ya ce wanda aka kama ya gaya wa yansanda cewa ya sha aikata laifin fashi da makami.
Ya ce an taba daure shi a Kurkuku tsawon watanni uku ba tara bayan ya aikata laifin sata.
Ya ce Yana da budurwa (Karuwa) a Unguwar Sabon gari Kano inda yake rayuwa da ita bayan mahaifinsa ya kore dhi daga gida sakamakon aikata laifin sace sace da mallakar bindiga.
Kalli bidiyon cikakken bayani:
0 Response to "Kasurgumin mai fashi da makami da 'yan sanda suka kama a Kano yayi Jawabi Cikin wannan Bidiyon >>>"
Post a Comment