--
An Fara Biyan Ma'aikatan N-Power Hakkokinsu N150,000

An Fara Biyan Ma'aikatan N-Power Hakkokinsu N150,000


Ma'aikar jin kai da walwala ta bayyana cewa ta fara biyan ma'ikatan N-Power na rukunin A da B, basukan da suke binta, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.


Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren dindindin na ma'aikatar, Bashir Alkali, ya fitar ranar Jumu'a a babban birnin tarayya Abuja.


Alƙali ya bayyana cewa tsarin biyan albashi na gwamnatin tarayya ya dakatar da asusun ma'aikatan N-Power 14,021 a shekarar 2020 bisa wasu dalilai. 


A cewar sakataren, daga cikin dalilin da suka haifar da haka sun haɗa da, ma'aikatan na amfani da asusu kala daban-daban wajen karɓar albashi da alawus daga ma'aikatun gwamnatin tarayya fiye da ɗaya. 


Sakataren yace yin hakan ya sabawa dokokin shirin N-Power kuma za'a iya kama mutun da zargin aikata cin hanci da rashawa. 


Bayan gano haka, wane mataki FG ta ɗauka? Bugu da ƙari Alkali yace ma'aikatar ta gudanar da bincike tare da haɗin guiwar ma'aikatun gwamnati kuma zuwa yanzun an gano ma'aikata 9,066 da suka dace a biya su kuɗaɗensu. 


"Bisa abinda muka gano, albashin waɗannan ma'aikatan N-Power da yakai N150,000 kowannen su ana cigaba da biyansu. Sun fara samun sakon karta kwana na shigar kuɗinsu cikin asusun su yau." "Za'a cigaba da rike kuɗaɗen sauran mutum 4,955 har sai an kammala gudanar da bincike nan gaba." 

0 Response to "An Fara Biyan Ma'aikatan N-Power Hakkokinsu N150,000"

Post a Comment