--
Bidiyon Ministan Tsaro Dauke da Bindiga Kirar Ak47 Yabar Baya da Kura

Bidiyon Ministan Tsaro Dauke da Bindiga Kirar Ak47 Yabar Baya da Kura


Domin Tabbatar Da Tsaro Badan Tsoro Ba.


Daga Abubakar A Adam Babankyauta. 


Mai girma ministan tsaron Nijeriya manjo janar Bashir salihi magashi dauke da bindigar shi kirar AK-47 Ayayin da zai fita zuwa wani uzirin shi. 


Kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana da cewa a karan farko an hango ministan tsaron Nijeriya manjo janar Bashir salihi magashi dauki da bindiga kirar AK-47 a cikin wani fefen bidiyo inda yan Nijeriya keta tofa albarkacin bakin su. 


Saidai da yawan yan Nijeriya na tofa albarkacin bakin su ne sakamakon ganin bai dace a ce ministan tsaro daukar bindiga kirar AK-47 ba


Wasu kuma na ganin cewa ministan ya dauki bindigar ne domin zaburar da yan Nijeriya akan su tashi su kare kan su.Toh koma dai menene munama mai girma ministan tsaron Nijeriya manjo janar Bashir salihi magashi kyakkyawan zato tare da tunanin cewa ministan ya dauki bindigar ne domin tabbatar wa da duniya cewa zai iya yakar yan ta,addan Nijeriya. 


Akar she ina rokon ubangiji Allah ya taimaki ministan tsaron Nijeriya manjo janar Bashir salihi magashi akan kyawawan manufufin shi na alkairi.

0 Response to "Bidiyon Ministan Tsaro Dauke da Bindiga Kirar Ak47 Yabar Baya da Kura"

Post a Comment