Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Gwamnatin Ganduje Duba dalili
Majalisar dokokin jihar Kano, ta amince da dakatar da gwamnatin Kano karkashin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, daga bada damar yin gine-ginen shagunan kasuwanci a babban masallacin Idi na Fagge (Masallacin Waje), bayan wani kuduri da dan majalisar jiha na Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa, ya gabatar yau a gaban majalisar.
Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, kudurin dan majalisar na karamar hukumar Dala, Lawan Hussaini, ya samu amincewa daga mafi yawan yan majalisun da suka halacci zaman majalisar a yau, wanda nan take aka umarci gwamnatin Kano da ta dakata daga wannan aiki.
Kudurin na zuwa ne kasa da awanni 24 da shugaban kwamitin amintattun masallacin, Sheik Tijjani Bala Kalarawi, yayi murabus daga mukaminsa, bisa yadda yace ana gina shaguna ana bawa wadanda ba ahalin addini ba, gashi kuma bazai iya dakatarwa ba, shi yasa ya sauki don bai san me zai cewa Allah ba, tunda dai Allah da kansa yace masallaci nasa ne.
Daga: Kano Online News
5/10/2021
0 Response to "Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Gwamnatin Ganduje Duba dalili"
Post a Comment