--
Ƙawayen Amarya Sunsa Ango Ya Saki Amaryarsa a Daren Farko duba yadda abun ya faru

Ƙawayen Amarya Sunsa Ango Ya Saki Amaryarsa a Daren Farko duba yadda abun ya faru


Wani Ango ne dai ya saki Amaryarsa saki ɗaya a daren da aka kawota tun kafin ya shiga ɗakin.


Hakan dai ya biyo bayan da ƙawayen Amaryar ne suka kulle ƙofa suka ce sam bazasu buɗe ƙofar ɗakin ba sai an biyasu kuɗin al'ada ta sayen baki har naira dubu ɗari biyu (₦200,000).


Da jin haka sai abokan Ango suka yi ta luguden laɓɓa da ƙawayen Amaryar don neman ayi musu sassauci. Bayan da Angon yaga abin ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa ga dare na ƙara tsawo ana ɓata lokaci tunda ƙawayen sun kafe kan sai an biya ₦200,000 yaga dai da gaske sukeyi, sai yace a basu naira dubu talatin (₦30,000).


Bayan an ƙidayo dubu talatin aka ce gashi su buɗe ƙofar sai kawai ƙawayen Amaryar suka ƙeƙasa ƙasa suka ce basu yarda ba, naira dubu talatin (₦30,000) tayi kaɗan. Don haka ba zasu buɗe ƙofar ba sai an ƙaro.


Daga nan sai Angon ya kira Amaryarsa a waya sau biyu, ita kuma taƙi ɗaga wayar Angonta.


Abinka da ƙaddara, aikuwa cikin fushi sai Angon ya ɗauki wayarsa ya turawa Amaryarsa saƙon karta-kwana wato (Text Message), cewa, 'Na sakeki saki ɗaya.


Kafin kace kwabo! Ƙawayen sun buɗe ƙofar kowa ta gudu gidansu suka bar Amarya da Sallallami cikin baƙin ciki.


Iyaye da Al'umma sai a ɗauki darasi!

0 Response to "Ƙawayen Amarya Sunsa Ango Ya Saki Amaryarsa a Daren Farko duba yadda abun ya faru"

Post a Comment