--
Wallahi aure nake so na gaji da kwana ni kadai – Cewar budurwa dake neman miji ruwa ajallo Kalli Bidiyon Ta Anan

Wallahi aure nake so na gaji da kwana ni kadai – Cewar budurwa dake neman miji ruwa ajallo Kalli Bidiyon Ta Anan


Budurwa ta koka kan yaddaa take matukar son aure amma babu wanda ya fito, ta dauki takaitaccen bidiyo ta wallafa a shafinta tana kuka…


Kamar yadda kowa ya sani yanzu mun shigo wani zamani da rayuwa tayi wahala, haka abubuwa na addini da al’ada na cigaba da canja a kowacce rana, hakan ya sanya al’umma da dama ke shiga cikin wani hali idan suka bukaci wani abu da zai sanya su jin dadin rayuwa suka rasa.


Samari da ‘yan mata da yawa a wannan zamani na bukatar aure, sai dai kuma wasu dalilai da dama na hana su ganin sun cimma wannan buri na su.


A lokuta da dama samari na samun matsalar aure sakamakon rashin aikin yi, rashin kudi da sauran su, yayin da su kuma mata a nasu bangaren sukan samu matsala sakamakon rashin hali, wasu kuma saboda ruwan ido da wani buri na abin duniya.


A wani bidiyo da jaridar mu taa Labarun Hausa ta ci karo dashi dake yawo a shafukan sadarwa ya nuna yadda wata budurwa ke rusa kuka tana bayyana irin yadda take son aure.


Bidiyon mai tsawon dakika 15 ya nuno budurwar mai suna @dinaouma1 a shafin tiktok cikin hijabi tana kuka tana cewa:


“Wallahi aure nake so, na gaji da kwana ni kadai”



Wannan bidiyo ya dauki hankula da yawa inda mutane da dama suka dinga yadawa a shafukan su, cikin mutanen da suka wallafa wannan bidiyo a shafinsu akwai, tsohon Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani. Sai kuma wani mai suna Muhammad T. Shehu, wanda ya wallafa yayi rubutu a kasa kamar haka:


“Jama’a dan Allah a samu wani ya auri wannan baiwar Allah mana…”



0 Response to "Wallahi aure nake so na gaji da kwana ni kadai – Cewar budurwa dake neman miji ruwa ajallo Kalli Bidiyon Ta Anan"

Post a Comment