--
Yadda Maryam Abubakar Matar Aure ke kwanciya (zina) da ɗan bindiga saboda talauci

Yadda Maryam Abubakar Matar Aure ke kwanciya (zina) da ɗan bindiga saboda talauci


Yadda Maryam Abubakar Matar Aure Ke Kwanciya Da Ɗan Bindiga, Sannan Takai Musu Wasu Matan Zuwa Cikin Daji Tare Sauran Ababen More Rayuwa.


A cikin shekara ta 2021 kadai, yan bindiga da ke ayyukan ta’addanci a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya musamman a yankin Arewa maso Yamma, sun kashe gomman mutane, tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira.


Ƴan bindigar sun kuma yi awon gaba da yara ‘yan makaranta da yawa, tare da neman kudin fansa domin sako su.


Ƴan bindigar sun kuma mayar da yankin ya zama wuri mafi rashin tsaro a kasar. Abin baƙin ciki, duk da haka, wasu matan da ya kamata su fahimci irin barnar da ƴan bindigar ke yi musamman yadda ayyuka ƴan bindigar suka shafi mata da yara, haka wasu matan irin su Maryam suka rufe ido suka cigaba da yi wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makaman aiki.


Wani abin damuwa ma shi ne, matar aure da ake tsammanin ta zama uwa ta gari, itace yanzu ta iya ƙulla yin soyayya da daya daga cikin yan bindiga dake dajin Kaduna, ta kuma wadata su da yan uwanta mata don jin dadi.


Idan ba a manta ba a safiyar yau ne wani rahoto da gidan Talabijin na Channels TV ya fitar, ya bayyana cewa kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya bayyana kama wata matar aure mai shekaru 39 mai suna Maryam Abubakar, wacce saurayinta dan bindiga ne duk da cewa tana da aure.


Rahoton yace, Maryam wadda mijinta yana raye kuma yana gida, tana saduwa da daya daga cikin ‘yan bindigar, tare da wasu matan sannan suna kai musu abinci, da kayayyakin more rayuwa da ‘yan mata don jin dadi.


Har ila yau, suna taimaka wa ’yan bindigar wajen gudanar da bincike, da kuma ba su bayanai kan wani abin da aka sa a gaba wanda yin haka hakika wannan wani zagon kasa ne ga yakin da gwamnati ke yi da rashin tsaro a kasar.


Mutane irin su Maryam Abubakar da ke aiki da ‘yan bindiga, ko dai a matsayin masu ba da labari, ko kuma masu kawo kayayyaki, suna zagon kasa a yakin da gwamnati ke yi da rashin tsaro a kasar.


Za a iya cewa, kayayyakin da mutane irin su Maryam suke kaiwa ƴan bindigar ne ya sa ’yan ta’addan masu dauke da makamai samun saukin rayuwa a cikin dajin.


Har ila yau, idan ba tare da bayanai da abubuwan da mutane irin su Maryam, da sauran masu ba da labari suka ba wa waɗannan ‘yan bindiga ba, ‘yan bindigar ba za su iya rayuwa ba na dogon lokaci a cikin daji.


#JaridarSokoto

0 Response to "Yadda Maryam Abubakar Matar Aure ke kwanciya (zina) da ɗan bindiga saboda talauci"

Post a Comment