--
Yadda Zaku Maida Layin Ku Na Mtn Data sim, Kuna Siyan Datan Mtn Welcome Back offer 1GB A N200 Kacal. Kubi ta wannan Adreshin dake kasa domin ganin yadda zakuyi

Yadda Zaku Maida Layin Ku Na Mtn Data sim, Kuna Siyan Datan Mtn Welcome Back offer 1GB A N200 Kacal. Kubi ta wannan Adreshin dake kasa domin ganin yadda zakuyi

 


Assalamu alaikum yan uwa barkan ku da wara haka da fatan kuna lafiya yau ba tare da bata lokaci ba ina tafe muku da hanyar da zaku maida layin ku na mtn ya dawo yadda zakuna sayan Mtn Welcome Back Data nasan dayawan ku sun san Welcome back Data wadan da basu sani ba ko kuma wadan suka manta zamu sake tunatar dasu.


Menene Mtn Welcome Back Data


Mtn Welcome back data wani tsari da mtn suke sakawa duk layin mtn da suka ga dama dan ba kowani layi ne yake yi ba kuma ba shigar sa akeyi ba baida code na shiga ko kuma wassu hanyar shigan sa mtn ne suke sa duk layin da suka ga dama.


Wannan tsarin Mtn Welcome Back Data zai baku dama ne kuna sayan Data me saukin gaske nasan dayawa daga cikin ku sunsan wannan tsarin indai layin ku yanayi a baya dan sanin kanku bayan wassu watanni mtn suna daina sayarwa masu sayan datan ma ana suna rufe wannan tsarin a layuka masu zamu nuna muku hanyar da zaku dawo da layin ku ku cigaba da saya idan kuma dama baka taba saya ba kaima zamu nuna maka haske.


Yadda Saukin Datan Mtn Welcome Back Yake.


Zasu baka daman sayan data me saukin gaske dan ba datar da ta kai wannan datar arha a yanzu haka.


1GB a naira 200 Yana Kwana 7


4GB A Naira 1000 Yana Kwana 30


2GB A Naira 500 Yana Kwana 7


250Mb A Naira 100 Yana kwana 3


Wadan nan sune saukin datan kaga ko sayan data zakayi gun masu sayarwa saika sayi 1gb a naira 300.


Yadda Zaku Maida Layin Ku, Kuna Sayan Datan Mtn Welcome Back Data.


Hanyar da zaku bi wajen maida layin ku na mtn kuna sayan Welcome Back Data hanyar guda daya ce kuma nima ita nabi kuma nayi nasarar dawo da layina wanda nake saya dashi a baya kuma ya tsaya amma yanzu ya dawo aiki.


Abu na farko da zakayi ya kasance kana da layin Mtn guda 2 ko 3 misali kanada layin ka na asali wanda kake amfani dashi saika samu wani layin mtn din nasan dayawa daga cikin ku kunada layin mtn sama da guda 1.


To idan ya kasance kanada nayin mtn guda 2 ko 3 to a cikin layin da ba asan ka dashi sosai ba ma ana bada shi kake amfani dashi gun kira da sauran su to wannan da baka amfani dasu din shi zaka sauke su daga cikin waya ka aje sa harna tsawon sati baka sa a waya ba to sati 2 na cika kadau wannan kasa a waya saika gwada sayan datar Mtn Welcome Back Data ta hanyar danna wannan Number *131*65# kana dannawa zaka ga yayi da yardar Allah ni haka nakeyiwa layukana da shike inada layin mtn guda 3 kuma sanin kanku wadan da suke amfani da wannan datar bayan watanni kamar wata 6 ko 7 zaku ga sun daina sayar muku to ni hikiman da nake musu asali layukana 2 ne da nake mafani dasu wajen sayan datan ina sauke daya daga waya na aje sai ina amfani da dayan to lokacin da wanda nake amfani dashi ya tsaya shima saina cire sa a wayan nasa wanda ya dade a ajen shima ina gwada sayan datan sai naga sun sayar min.


Wannan layi danake amfani dashi yanzu kwata kwata sati 2 da aje sa amma yanzun suna bani damar sayan datar kamar yadda zaku dani a hoton kasa.


Indai kunbi wannan hanyar dana kawo muku insha allahu kuma zaku maida layin ku ya dawo yana saya.


Ku sani kuma mtn basu bada daman sayan datan nan a layin da aka fiye amfani dashi ma ana layin da koda yaushe yana cikin waya.

Idan Allah yasa a cikin ku akwai wanda yakeda layin mtn daya dade a aje to yasa a waya yanzun nan ya danna *131*65# zaku ga ya nuna muku adadin datar saiku zabi wanda kuke so ku saya insha allahu zai dace.

Zaku iya turawa abokan ku da sauran su


SOURCE: https://lastng.com/

0 Response to "Yadda Zaku Maida Layin Ku Na Mtn Data sim, Kuna Siyan Datan Mtn Welcome Back offer 1GB A N200 Kacal. Kubi ta wannan Adreshin dake kasa domin ganin yadda zakuyi"

Post a Comment