--
Jarumar Kannywood Aisha Tsamiya zata yi Aure a ranar Juma'a mai zuwa

Jarumar Kannywood Aisha Tsamiya zata yi Aure a ranar Juma'a mai zuwa




Fitacciyar Jarumar a Masana’antar shirya wasan fina-finan Hausa na Kannywood Aisha Aliyu wadda aka fi sani da “Aisha Tsamiya” za ta yi aure.

Labarin ya bayyana ne a wani katin ɗaurin aure da shafin “Kannywood Celebrities” ya wallafa a Facebook da kuma Instagram.

Katin wanda ya fara yawo a kafafen sada zumunta ya nuna za a ɗaura auren jarumar a ranar Juma’a wato jibi kenan 25/2/2022 a Masallacin Sheikh Zarban, da ke Unguwar Ƴan Kaba Kwanan Ƴan Wanki kusa da gidan Tanko Yakasai bayan Sallar Juma’a.

Katin ya bayyana sunan wanda zai auri Jarumar da Alhaji Buba Abubakar.

Jarumar dai ta jima ba ta fita fitowa a sabin shirin fina-finai ko da a irin na “series” mai dogon zangon nan da ake yayi yanzu kuma bata sanar da ficewa ba daga masana’antar. Ta maida hankali kan kasuwancinta na sayar da kayan kwalliya da gyara jiki.

Sai dai mun yi ƙoƙarin tuntubar Jarumar amma layinta kashe sannan mun ƙira layin wata makusanciyarta ma ita ma wayarta a kashe.

Jaruma Aisha Tsamiya za ta amarce ranar Juma’a.

0 Response to "Jarumar Kannywood Aisha Tsamiya zata yi Aure a ranar Juma'a mai zuwa"

Post a Comment