--
Tirkashi, za a fara binciken dalilin mutuwar shugaban kasar Libya Gaddafi

Tirkashi, za a fara binciken dalilin mutuwar shugaban kasar Libya Gaddafi





Cikin Fushi Da Bacin Rai, Shugaban Rasha Vladimir Putin Ya Nemi Kungiyar Kasashen Turai (NATO) Da Su Fada Masa Dalilin Kisan shugaban Kasar Libya Ghaddafi 




A cikin wani faifan Bidiyo na shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa kungiyar NATO kungiya ce ta kasashen Amurka, Ingila, da Faransa da kawayen su wadanda su ke yaki ta hanyar zalunci da danne kasashen da ba su kai karfin su ba.


"Miye dalilin ku na kashe shugaban kasar Libya Muhammadu Al-Ghaddafi?"


"Na sani cewa kun kashe shi ne saboda ya ki bin ku ne, saboda ya ki mara muku baya wajen ganin kun shigo kasar sa kun cutawa al'ummar sa".


"Kun kashe shi, kun lalata kasar sa, kun kwashe dukiyar kasar sa saboda zalunci".


"Wannan shine irin zaluncin da kungiyar NATO kuke aikatawa kasashen duniya musamman na Afriaca". 


"Ghaddafi shugaba ne mai son kasar sa da cigaban ta, amman kun kashe shi akan zalunci kun kwashe dukiyar kasar"Inji shi


Daga: S-bin Abdallah Sokoto

0 Response to "Tirkashi, za a fara binciken dalilin mutuwar shugaban kasar Libya Gaddafi"

Post a Comment