--
‘Yan Sanda sun kama wani Mutum da ya yaga Qur’ani Mai Girma a jihar Kano

‘Yan Sanda sun kama wani Mutum da ya yaga Qur’ani Mai Girma a jihar Kano


Wani matashin jami’in tsaro da har yanzu ba a san sunansa ba, a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda a Kano bisa zarginsa da yaga da taka wasu sassa na Alkur’ani mai girma.

Wanda ake zargin mai kimanin shekaru 20 a duniya, an ce jami’an hukumar Hisbah sun ceto shi daga hannun al’ummarsa a unguwar Kuntau da ke cikin birnin Kano.


Daga nan kuma aka mika shi ga ‘yan sanda kuma a halin yanzu yana tsare tare da gudanar da bincike a hannun Yan sanda.


Wani dan uwa mai gidan da wanda ake zargin ke aiki mai suna Sunusi Ashiru ya shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa matashin ya tsira da ransa.


Ya ce: “Ban nan lokacin da ya yi hakan amma na dawo na ga mutane da makamai iri-iri suna kokarin kashe shi.


“Lokacin da na tambaye shi, sai suka bayyana abin da ya yi kuma a lokacin ne jami’an Hisbah suka kubutar da shi, daga bisani suka mika shi ga ‘yan sanda.”


Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.


Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda.


Ya yi alkawarin yin cikakken bayanin akan abin da ya faru da kuma ci gaban da binciken abun da ya faru.

- Demokuradiyya

0 Response to "‘Yan Sanda sun kama wani Mutum da ya yaga Qur’ani Mai Girma a jihar Kano"

Post a Comment