--
Za mu yi kasuwanci amma muna bukatar jari – Martanin Matasan Najeriya ga Pantami

Za mu yi kasuwanci amma muna bukatar jari – Martanin Matasan Najeriya ga Pantami



Ministan da yai kaurin suna wajen kuka, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sha suka a kafafen yada labarai biyo bayan kalamansa na shawartar matasan Najeriya da su mayarda hankali kan kasuwanci maimakon neman aikin gwamnati.

Yusuf Saidu Maza ya ce, "Ya kai Minista, ina so daga cikin albashinka na wannan wata ka saka mini jari saboda matsalata ce, Allah Ya saka maka da alheri."

"Mungode da wanga shawara.

Dan Allah Mallam wane kasuwanci kai Nima naje nariqemai wuta? ". Inji Muhammad Abubakar Abdullahi

"Wane kokari kukayi na rage hauhawar kayan masarufi kasuwanci ma ya karye komai haraji haraji ribar kurarriya ce gamu masu karamin jari". Inji Ibraheem Kabyr


"To Dr. Amman banji kayi magana akan jarin da matasan zasuyi Sana'arba wannan da suna samun hakan wallahi wani ko anbashi aikin Gwamnatin bazaya karɓaba". Inji Shehu Tanimu Lomolo 


"Allah yabawa kowa hanya da zai rufawa kansa asiri,idan ta fannin kasuwanci ne kokuma ta fannin aikin gwamnati,hakanan wadansu lokutan sai kaga samun jarin da talaka zai rufawa kansa asiri sai ya gagareci kudi kuma sunyi tsadan samu Allah yabawa kowa hanya dazai rufawa kansa asiri hanya mafi alkairi,sannan kuma gwamnati sai kun taimaka sannan talaka yajidadi bawai haka kawai zaku yita fadin abinda kukeso, abinci yayi tsada yakamata ba kuduba wane irin hali da yan nageria sukeciki Allah yakara mana lafiya da binda lafiya katashi". Inji Barde Barno

0 Response to "Za mu yi kasuwanci amma muna bukatar jari – Martanin Matasan Najeriya ga Pantami"

Post a Comment