--
Abin Al'ajabi:- Mun wayi gari da Mutuwar wani Bawan Allah Yayin da ya mutu bayan Yayi Sujjada Ga Allah a Cikin Sallah

Abin Al'ajabi:- Mun wayi gari da Mutuwar wani Bawan Allah Yayin da ya mutu bayan Yayi Sujjada Ga Allah a Cikin Sallah


 Wata HIKAYAH mai dauke da darasi game da Zaman Duniya


Kashi na daya:


Wani matashi karimi mutumin kauye, ya kasance tare da mahaifiyarsa kadai ba shi da uba, sau da yawa takan ce masa kada ka yarda ka yi abuta da *"mai niyya biyu"*, duk sa'ar da ya ji ta ce masa haka sai ya ce: to kuma ya zan yi in san shi? Sai ta ce masa: indai shi ne to zai fada maka da bakinsa!


A kwana a tashi rannan sai mahaifiyarsa ta rasu, ya zauna bayan ranta shi kadai a gida babu walwala da nishadi, babu mai bashi shawara a rayuwarsa. 



Sai kurum ya yanke shawarar sayar da gidansu ya shiga duniya, domin kuwa zamansa a garin yana jefa shi cikin damuwa. 


Daga karshe ya sayar da gidannsu ya sayi rakumi da makamin fada saboda hatsarin daji, sauran kudinsa kuma ya daure su a cikin tsumma ya dannan su cikin kayansa, sannan kuma ya dorawa rakuminsa kayan ya yi addu'a shima kuma ya hau. 


A kwana a tashi yana cikin tafiya har ya fita daga yankinsu ya shiga SAHARA, bai yi nisa ba sai ya gamu da wani abin al'ajab! Mutum a kwance cikin jini yana kusa da mutuwa, an karya masa kafa, sannan ga zazzafar kishirwa tana azabtar da shi. 


Ko da wannan karimin bawan Allah ya ga haka sai ya diro daga kan rakuminsa ya rungume shi yana karkarwa, ya ce malam lafiya?! 



Cikin gaggawa ya bashi ruwa, ya yaga rawaninsa ya daure masa kafarsa karyayya, ya goge masa jini da kuma kasa, sannan ya dora shi bisa rakumi ya hau suka ci gaba da tafiya. 

Wannan matashi ya dubi wannan bawan Allah cikin tausayi, idonsa cike da hawaye ya ce: malam fada mani abinda ya faru da kai? 


Sai wannan mutumin ya juyo da fuskarsa kadan ya ce masa: ai yaki ne ya hada mu da wata kabila, daga karshe suka yi nasara a kan kabilarmu, suka kashe wasu sannan suka kame wasu, tsammanin ba zan rayu ba suka jefar da ni a hanya suka yi gaba da sauran, musamman ganin cewar a karye nake, to shi ne cikin taimakon Allah basu jima da bacewa ba sai na hango ka ka tunkaro inda ka same ni... Ya ce wannan shi ne takaitaccen labari na, kaima don Allah bani labar

0 Response to "Abin Al'ajabi:- Mun wayi gari da Mutuwar wani Bawan Allah Yayin da ya mutu bayan Yayi Sujjada Ga Allah a Cikin Sallah "

Post a Comment