--
ABINDA WANI UBA YA FADAWA 'YARSA ANA GOBE ZA'AYI AUREN TA

ABINDA WANI UBA YA FADAWA 'YARSA ANA GOBE ZA'AYI AUREN TA


 ABINDA WANI UBA YA FADAWA 'YARSA ANA GOBE ZA'AYI AUREN TA


'Yata, gobe zaki daina amsa sunarki na 'yata. Zakiyi auren farin ciki zaki auri muradin ranki wanda kike kauna.


Kada kiyi kewata domin na cika burina na aurar dake ga wanda kike kauna, yanzu kuma ya rage naki ki cika naki burin. 


Daga yarintarki, na samu nabaki tarbiya cikin ikon Allah ko? Kafin ki amsa mini da cewa eh, akwai wani abinda nakeso na fada miki dangane da zama da mijin aure na kasancewarki matar aure. 


Kina tuna lokacin da kika rubuta jarabawar WAEC da JAMB? Kinzo kinsameni na baki #20,000 na registration? Duk da cewa na baki, toh kudin ba nawa bane. Nasan kin dauka cewa ni na biya miki kudin. Maganar gaskiya shine lokacin bani da sisi, Mahaifiyarki ita tabani. Tanada damar da zata baki kudin da hannunta, amma sai ta bani ni na baki. Ki zamto mai tallafawa mijinki. Wani lokacin rayuwa takan tsananta, mijinki zai iya zamowa a fusace, domin rayuwa tayimar daurin tamtam, zai iya jin tsoron kada ya rasaki domin abin hannunshi ya kare a wannan lokacin, toh a wannan yanayi ne yake bukatar tallafinki, ki zamto mai bashi karfin guiwa sosai. 


Babban hanyar da zaki bi wajen nunawa mijinki kina kaunar shi shine kina girmamashi da kuma kuma girmama ra'ayinshi!. 


Ta yiyu kuyi jayayya tsakaninku, ko kuma kiki aminta da ra'ayinshi, amma a karshen ranar ki nunamar cewa ya cancanci ki girmamashi. Kina tuna lokacin da nayiwa Mahaifiyarki tsawa? meye tayi lokacin? Shiru tayi.Kina kuma iya tuna wani lokaci data mini tsawa? Meye nayi? Shiru nayi nima lokacin. 


Yake 'yata, ki zamto mai shiru ga mijinki lokacin da yayi fushi. Lokacin da dayanku zuciyarsa ke tafasa, dayanku ya tabbata zuciyarsa tana sanyaye. Idan ma'aurata biyu dukkansu suna tsawa wa juna a tare, ananne babbar matsalar aure ke somawa. 


Farkon abinda yakamata kisani dangane da mijinki shine abincin dayafi so! Idan sunada yawa, ki tabbata kin rikesu a ranki. Kada kibari sai ya roka kimar, ki zamto kinayi ba sai ya nema ba. 


Akwai wani lokacin da Mahaifiyarki ta kamani ina wasa da hannun wata mata, tabbass matar ta janye hankalina amma bawai ina cheating din mahaifiyarki bane. Lokacin data ganmu, batayi fada da matar ba, kawai kama hanyar ta tayi ta wuce batace uffanba. A ranar naji tsoron komawa gida domin ina tsoron abinda zan tarar a gidan idan na koma. Ammana sai nayi ta mazan na koma gida. Kuma wallahi batace uffan ba. Ta hadamin abinci kamar yadda ta saba. A hakan a tsorace nake domin nasan abinda na aikata. Sai na fara bata hakuri ta kuma ce babu komai ya wuce. Daga wannan rana ban sakewa yiwa wata mace kallo na biyu ba. 


Waye yasan meye zai faru da ta yimin masifa ta balbaleni? Watakila dana fita na bar mata gidan na koma wajen waccan matar data kamani da ita. 


Wani lokacin shiru kan zamo silar sulhu maimakon fada da masifa da balbalin bala'i. Ki manta da wadancan littattafan na soyayya da kike karantawa lokacin kina budurwarki. Kin tuna wadannan finafinai na soyayya na India da American? Wasu Nollywood Movies dinnan? Ki manta dasu, kada ki tsammanin rayuwar aurenki ya zamto irin wadancan. 


Rayuwa a zahiri ba kamar wacce wasu Directors da marubuta, su Artist da Producers suka rubuta bane, rayuwar aure Allahu Jalla Wa Azza ne ya ke Directing kuma shine Producer, shine Artist.


Abu na karshe dana bukata kisani shine....... Kina tuna lokacin da aka haifeki? 


Bayan aure na da Mahaifiyarki, rayuwa ta tsananta garemu. Mamarki ayyuka biyu takeyi domin ta tallafa mana, bawai bana aiki bane, nima ma'aikaci ne. Ina dawowa gida karfe 6 na yamma, ita kuma karfe 8 na yamma kuma a gajiye. A hakan bata ta6a hanani abincin dare ba ko kuma kin kulawa da wajen kwanciyar mu. A hakan aka samu aka haifeki cikin ikon Allah. 


Kada ki kuskura ki hana mijinki kanki ko abinci komai gajiyanki, ki zamto mace tagari.


Har abada kinanan a 'yar Daddy.

0 Response to "ABINDA WANI UBA YA FADAWA 'YARSA ANA GOBE ZA'AYI AUREN TA"

Post a Comment