--
Bello Turji ya saki bidiyon Sabbin Makaman da suka Mallaka

Bello Turji ya saki bidiyon Sabbin Makaman da suka Mallaka


 

Gawurtaccen dan bindiga Bello Turji ya saki sabon Bidiyo inda yake nunawa Gwamnatin Najeriya manyan makaman da yake da su na yaki


Kasurgumin dan ta’adda, Bello Turji, ya ce a shirye yake ya nuna wa gwamnati wasu mayanka da ake yanka ’yan uwansa a yankin da yake.


A hirarsa da Aminiya a maboyarsa, Turji, wanda ya fitini jihohin Zamfara da Sakkwato, ya ce akwai mahauta akalla guda biyu da aka ware domin yanka ’yan uwan sa Fulani, amma gwamnati ba ta sani ba.


Ya yi ikirarin cewa tausayin talakawa da jami’an tsaro su ke kashewa ne ya sa shi rubuta wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasikar neman zaman lafiya.


A cewarsa, a baya gwamnati ta yaudare su, ta sa jami’an tsaro sun kashe su, bayan ta sa sun lallashi yaransu sun mika mata makamansu da sunan zaman lafiya.


Amma duk da haka, sun zura ido su gani ko a wannan karo ko za ta cika alkawarin da ta yi musu domin samun zama lafiya.

0 Response to "Bello Turji ya saki bidiyon Sabbin Makaman da suka Mallaka"

Post a Comment