Bello Yabo karya yakemin bamu hadu a kurkuku ba - Bello Turji
Gawurtaccen Dan ta'addan nan nan jihar Sokoto, wato Bello Turji ya yi martani ga Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheik Bello Yabo, akan cewa sun hadu a Gidan Yari, Sannan yace karya ne basu hadu ba.
Ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya saki, inda ya kara da cewa su musulmai ne kuma suna salla, Sannan yana tsoron allahn da ya halicceahi shiyasa.
A kwanaki dai ne Malam Bello yabo ya bayyana cewa Turji sun hadu dashi a Gidan Yari, Sannan ya yi Masa nasiha.
Sai dai Bello Turji bai yi wata-wata ba inda ya mayar Masa da kakkausan martani.
Yace shi ba a taba kaishi a Ofishin yan Sanda ba mai, balantana Gidan kurkuku.
0 Response to "Bello Yabo karya yakemin bamu hadu a kurkuku ba - Bello Turji"
Post a Comment