--
SU WAYE MASU MUNANA FAHIMTA GA MALAM  PART 1...?

SU WAYE MASU MUNANA FAHIMTA GA MALAM PART 1...?


SU WAYE MASU MUNANA FAHIMTA GA MALAM? 

                          PART 1

Ya yan'uwa masu albarka ya kamata mu fahimci cewa shi wa'azi manufarsa ita ce tunatar da al'umma, dagane da Wani kuskure da suke aikatawa ko fadakar da su don kada su aikata shi a gaba, da kuma kwadaitar da su bisa aiyukan da'a. 

Addinin musulunci ya bayyana hanyoyin yin wa'azi(أساليب الوظ),  malaman tafseer sunyi bayani Mai gamsarwa kan fadin Allah madaukakin sarki

 {ادْعُ إِلَى سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ }النحل 125

kuma sun bayyana  hanyoyin yin wa'azi, sun kuma bayyana manufar wa'azi,.  ga maganar wasu daga cikin malaman musulunci :-


a) ibnul kayyim ya bayyana ma'anar wa'azi acikin littafinsa: tafseerul qayyim da cewa "الأمر والنهي المقرون بالترغيب والترهيب"

wato "wa'azi shi ne: Umarni da kuma Hani ta hanyar kwadaitarwa da kuma tsoratarwa"


b) Muhammad Rashid ridha a cikin littafinsa tafseerul mannaar"الموعظةإسم من الوعظ أي: الوصية بالحق    والخير، واجتناب الباطل والشر، بأساليب الترغيب، والترهيب التي يرق لها القلب، فتبعث على الفعل والترك


" wa'azi shi ne :yin wasiyci da Gaskiya da kuma ayyukan alkairi da kuma nesantar mummunan aiki da na sharri ta hanyar amfani salon kwadaitarwa da tsoratarwa, wadda zai ta tausasa zuciya,ya kuma zaburar da ita izuwa ga aiki (na alkairi) da kuma barin aikata mummunan aiki "

wadannan maganganun na malamai da muka kawo gaba daya su na bayyana mana cewa ya halatta Mai da'awa ya yi amfani da salon ya ke ga zai fadakar da al'umma, dagane da Munin abunda ya ke yi musu wa'azi a Kai.

don haka usulubin da sheikh AMINU IBRAHIM DAURAWA ya yi amfani da shi domin Yi wa mutanen da suke aikata Zina wa'azi ta hanyar bayyana abunda ya ke halakar da su  a matsayin shi ne abu mafi muni a jikin mace to  lalle Babu Wani kuskure a ciki.

To wannan maganar da malam ya fada  take ta trending a social media, Wanda wadansu da zamu iya cewa  ba su da gadon Kai (saurin FAHIMTA ) su ke munana FAHIMTA ga MALAM ,   to ba komai ne ya haifar da haka ba sai wadansu dalilai da za mu kawo a rubutu na gaba part 2 inshaa Allah

0 Response to "SU WAYE MASU MUNANA FAHIMTA GA MALAM PART 1...?"

Post a Comment