--
[BREAKING NEWS]:-Amurka Ta Bayyana Sunayen 'Yan Najeriya 6 Masu Taimakawa Kungiyar Boko Haram

[BREAKING NEWS]:-Amurka Ta Bayyana Sunayen 'Yan Najeriya 6 Masu Taimakawa Kungiyar Boko HaramGwamnatin kasar Amurka ta bayyana sunaye 6 na wasu ‘yan Najeriya a matsayin wadanda aka gano suna tamaka wa kungiyar Boko Haram Cikin mutanen da ka bayyana akwai Abudurrahman Ado Musa, Muhammad Ibrahim Isa, Bashir Ali Yusuf, Ibrahim Ali Alhassan, Surajo Abubakar Muhammad da Salihu Yusuf Adamu Kamar yadda bayanai suka nuna, an shigar da sunayen su cikin kundin masu taimaka wa ayyukan ta’addanci bisa umarnin shugaban kasar


Amurka - Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana sunayen ‘yan Najeriya guda 6 masu taimaka wa kungiyar ta’addanci ta Boko Haram da ayyuka na musamman da kuma kudade, VOA ta ruwaito. Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana yadda sashin kulawa da kadarorin ketare na Hukumar harkokin kudade na kasar Amurka, ta fitar da jerin sunayen. 


A sanarwar da ta fitar ranar Juma’a, cikin wadanda sunayensu suka bayyana akwai Surajo Abubakar Muhammad, Abdurrahman Ado Musa, Ibrahim Ali Alhassan, Salihu Yusuf Adamu, Muhammad Ibrahim Isa da Bashir Ali Yusuf.


Kamar yadda sanarwar ta nuna bisa ruwayar VOA, wadanda sunayen nasu ya bayyana suna amfani da hanyoyi da dama wurin hidimta wa kungiyar ta fannoni na fasahohin zamani.


Sanarwar ta nuna yadda sunayen suka shiga kundin masu tallafa wa ayyukan ta’addanci, bisa umarnin shugaban kasar na 13224.

0 Response to "[BREAKING NEWS]:-Amurka Ta Bayyana Sunayen 'Yan Najeriya 6 Masu Taimakawa Kungiyar Boko Haram"

Post a Comment