--
Karin Bayani: An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace

Karin Bayani: An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace


 Karin Bayani: An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace

An tsinci daya daga cikin 'ya'yan Farfesa Ali Isa Pantami, Al'amin Isa Ali Pantami a Dambam, Jihar Bauchi awanni bayan masu garkuwa sun sace shi Majiyoyi sun tabbatar da afkuwar lamarin amma ba su bayyana ko an biya kudin fansa ba kafin sako shi, ko ba a biya ba Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ba a kai musu korafi kan lamarin ba


An ceto dan ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Ali Isa Pantami, da aka rahoto cewa an sace shi a jihar Bauchi, Daily Trust ta rahoto. A cewar majiyoyi, an gano dan ministan ne a Dambam, daya daga cikin kananan hukumomin jihar Bauchi a ranar Juma'a a shigen jami'an tsaro


An Gano Dan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace


Majiyar ba ta bayyana ko an biya kudin fansa ba. Al'amin Isa Ali Pantami yana zaune ne tare kakansa Daily Trust ta tattaro cewa, wanda aka sace din, mai suna Al'amin Isa Ali Pantami, yana zaune ne tare da kakansa. Da ya ke tabbatar da sako shi, daya daga cikin masu kula da shi ya ce: "Yanzu muka baro gida; yana gida a yanzu. An gano shi a Dambam, inda wadanda suka sace shi suka ajiye shi. Sun sauke shi a wani shinge daga nan aka kawo shi gida." Da aka tuntube shi a ranar Juma'a, babban limamin masallacin Isa Ali Pantami, Imam Hussaini, wanda da farko ya ki cewa komai game da lamarin, ya shaida wa Daily Trust cewa "Yaron yana gida."


Be the first to get hottest news from our Editor-in-Chief SIGN UP THANK YOU! Check your email and confirm your subscription You are already subscribed to our newsletter! Check your inbox to be the first to know the hottest news Home Labarai LABARAI 'Karin Bayani: An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace Jummaʼa, Maris 25, 2022 at 5:02 Yamma by  Aminu Ibrahim An tsinci daya daga cikin 'ya'yan Farfesa Ali Isa Pantami, Al'amin Isa Ali Pantami a Dambam, Jihar Bauchi awanni bayan masu garkuwa sun sace shi Majiyoyi sun tabbatar da afkuwar lamarin amma ba su bayyana ko an biya kudin fansa ba kafin sako shi, ko ba a biya ba Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ba a kai musu korafi kan lamarin ba DUBA NAN: Danna “See First” karkashin karkashin "Following “ don samun labaran Legit.ng a shafinka na Facebook akai-akai Jihar Bauchi - An ceto dan ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Ali Isa Pantami, da aka rahoto cewa an sace shi a jihar Bauchi, Daily Trust ta rahoto. A cewar majiyoyi, an gano dan ministan ne a Dambam, daya daga cikin kananan hukumomin jihar Bauchi a ranar Juma'a a shigen jami'an tsaro. 


READ ALSO Osinbajo: Duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin Musulunci ne, MURIC An Gano Dan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Da mutane sun sace Al'amin Isa Ali Pantami yana zaune ne tare kakansa Daily Trust ta tattaro cewa, wanda aka sace din, mai suna Al'amin Isa Ali Pantami, yana zaune ne tare da kakansa. Da ya ke tabbatar da sako shi, daya daga cikin masu kula da shi ya ce: 


"Yanzu muka baro gida; yana gida a yanzu. An gano shi a Dambam, inda wadanda suka sace shi suka ajiye shi. Sun sauke shi a wani shinge daga nan aka kawo shi gida."


Da aka tuntube shi a ranar Juma'a, babban limamin masallacin Isa Ali Pantami, Imam Hussaini, wanda da farko ya ki cewa komai game da lamarin, ya shaida wa Daily Trust cewa "Yaron yana gida."


READ ALSO Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu Rundunar yan sandan Jhar Bauchi ta ce ba a kai mata korafi game da sace Al'amin ba Amma, kakakin yan sandan jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ba a kai musu korafi kan lamarin ba.


Wakilin Daily Trust ya nemi ji ta bakinsa game da garkuwar. "Abin da muke so daga mutane shine su taimaka mana da bayanai masu amfani kan mutanen da ba a yarda da su ba domin mu dauki mataki, kuma idan akwai wata matsala, a kai wa yan sanda rahoto." 


Batun garkuwa da mutane ya yi wa al'umma katutu, an sha kira ga gwamnati ta dauki matakan kawo karshen matsalar.

0 Response to "Karin Bayani: An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace"

Post a Comment