--
Kalli bidiyon yadda aka watsa miliyoyin kudi a bikin Maishadda

Kalli bidiyon yadda aka watsa miliyoyin kudi a bikin Maishadda


 


A ranar Lahadi 13 ne aka daura auren Babbak Furodusan Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda da Amaryarsa Husaina, Wanda aka daura a Masallacin Juma'a da ke jihar Kano.


Tun ranar Alhamis dai ne aka fara shagulgula na wannan biki, inda jarumai da dama suka hallara domij tayashi murna da zuwan wannan rana.

Manyan jarumai ne suka samu hallara daurin Auren, Wanda suka hada da Ali Nuhu, Mawaki Dauda Kahutu Rarara, Adam A Zango, Umar M Sharif da dai sauran jaruman Kannywood.


An lika masu kudade Masu yawa a wajen dina ta bikinsu, inda aka dauki bidiyon yadda ake watsa dubban miliyoyi a wajen walimai.

0 Response to "Kalli bidiyon yadda aka watsa miliyoyin kudi a bikin Maishadda"

Post a Comment