--
Kashe miji ba maslaha bane, rashin Imani ne da hauka, Cewar Fauziyya D Sulaiman

Kashe miji ba maslaha bane, rashin Imani ne da hauka, Cewar Fauziyya D SulaimanFitacciyar Marubuciyar nan da harshen Hausa wato Fauziyya D Sulaiman, ta bayyana cewa kashe Mijin Aure ba Maslaha bane ga ‘ya‘ya Mata, tace hakan hauka ne da rashin Imani.

Ta bayyana haka ne a shafinta na sada zamunta na Manhajar Facebook a yau Talata.


“A Shawarata, idan namiji  Allah ya hore masa abun da zai iya rike mace fiye da daya, ya kuma yanke shawarar kara aure ya fuskanci jarabar matarsa za ta iya halaka shi, Ko za ta iya illata shi,  yafi masa sauki ya sawwake mata ya huta, domin irin wadannan matan suna nuna halinsu tun kafin akai ga hakan, yanzu kamar wacce ta kashe mijinta ta Maraba an ce ta yi yunkurin kashe na farkon ya saketa, ta kuma taba kokarin cakawa facalarta wuka, lafiyarka da rayuwarka sun fi maka komai dan'uwa.

 

“Idan kuma ya zabi zama da ita saboda soyayyarta ko wani abu to ina bashi shawara ya hakura da karin auren kawai, amma muddin yasan zai kara auran ta saka shi a masifa irin wannan rabuwa da ita ya fi alkairi.


“Kullum ina fadawa mata karin aure Halal ne kuma har duniya ta nade ba zaa daina ba, idan mijinki ya dauke duk nauyin da Allah ya dora masa akanki na ciyarwa shayarwa da muhalli sannan ya yi adalci kamar yadda addini ya gindaya, ki yi hakuri ki zauna da abokiyar zamanki watarana sai labari, idan kuma kinga kina da kishin da ba za ki iya zama ba ki nemi ya sawwake miki cikin mutunci ki huta, amma kisa ko rauntawa ko illatawa ba mafita ba ce, za ki saka kan ki da yaranki da dukkan danginki cikin masifar da har abada ba za ku fita ba.

“Sannan an san soyayya ke saka kishi, amma ta yaya zaka cutar da abun da ka ke kauna don Allah?


“Nasan kishi abu ne mai za fi, amma mu dinga jin tsoron Allah,  shi tsoron Allah shike hana zuciya aikata mugayen abubuwa, Allah ya gafartawa bawan Allah da aka kashe, muna kuma kira ga hukumomi a tabbatar da yiwa wannan bawan Allah adalci ta hanyar hukunta wannan baiwar Allah daidai da abun da ta aikatawa mutumin da bai ji bai gani ba, Allah ya sa mu dace amin.

0 Response to "Kashe miji ba maslaha bane, rashin Imani ne da hauka, Cewar Fauziyya D Sulaiman"

Post a Comment