YANZU-YANZU| Wani ya rasu a yayin da yake sallah, a Massalacin. Umar bin Kattab, dake shatatalen Dangi, a jahar Kano.
Innalilahi wainnailahi ilaihi rajeun.
YANZU-YANZU| Wani ya rasu a yayin da yake sallah, a Massalacin. Umar bin Kattab, dake shatatalen Dangi, a jahar Kano.
Matashin ya gamu da ajalinsa ne a yayin da a katafi sujjada, inda kowa ya dago Amma shi ba dago ba, Bayan an idar da sallah a kaduba a katarar Rai yayi halinsa.
Allah ubangiji yajikansa, Allah yasa Aljanna ce Makomarsa, idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani
Daga Abdurrashid Abdullahi Kano
Ya Ilahee 😭😭😭
Yayin da sojojin Najeriya ke shirin janyewa daga kauyen Shimfida dake karkashin Karamar hukumar Jibia a jihar Katsina, sai mazauna yankin suka roke su dasu basu wasu 'yan mintuna domin su tattara kayansu da iyalansu suma su bar garin domin tsira da rayukkan su.
Shaidun ganin da ido sun tabbatar da cewa a lokacin 'yan ta'addar sun fara daukar matakai na labewa a sako da lungu dake Hanyar garin.
Daidai lokacin da sojoji suka bar garin, sai kawai 'yan bindiga suka fara harbi, hargitsi ya biyo baya, sakamakon haka yara 8 suka rasa rayukansu.
A halin yanzu sama da mutane 5,000 ne suka rasa matsugunansu da gidajen su, sannan sun kone musu abinci.
Yayinda mutane suka tarwatse zuwa neman tsira, wata mata mai juna biyu da ke gab da naƙuda an bar ta nan daga ita sai wasu mutane naƙasassu da tsofaffi sakamakon basu da karfin gudu, wadanda abin ya shafa su kuma sun samu mafaka a wata makarantar firamare cikin ajujuwa.
Saboda sanyi kuma yara ƙanana da tsofaffi sune ke cikin ajujuwa, sauran mutanen suna a waje, dalibban dake karatu a makarantar kuwa, an tilasta musu komawa daukar darasi a waje, akwai karancin abinci, ruwan sha, tabarmi da barguna a sansanin na wucin gadi.
Yanzu haka ‘yan bindiga sun mamaye kauyen Shimfida, su suke rike da iko a kauyen. 'yan bindiga kuma sun karbe hanya daya tilo dake zuwa garin.
Wadannan mutane suna buƙatar tallafi na gaggawa na ababen more rayuwa, abinci, kiyon Lafiya da addu'oi.
Allah SWT Ka jibanci al'amarin bayinka raunana.
0 Response to "YANZU-YANZU| Wani ya rasu a yayin da yake sallah, a Massalacin. Umar bin Kattab, dake shatatalen Dangi, a jahar Kano."
Post a Comment