--
Abin Takaici Ne Yadda Jama’a Ke Mana Kallon Ɓarayi – Gwamna El Rufa’i

Abin Takaici Ne Yadda Jama’a Ke Mana Kallon Ɓarayi – Gwamna El Rufa’i




Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, a ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, ya bayyana cewa mafi akasarin mutane na yiwa Gwamnoni kallon barayi marasa amfani.


Ya yi wannan furucin ne a shirin Sunrise Daily na Channels TV, yayinda yake amsa wata tambaya game da dalilin da yasa yake ganin zama gwamna ne aiki mafi wahala a Najeriya.


El-Rufai ya ce ya gano hakan ne a lokacin da yayi kan mulki.


“Mun hau kujerar mulki a lokaci mafi muni ta bangaren tattalin arziki. Mun zo a lokacin da farashin man fetur ke ruguzowa sannan mun gaji tsari da yake tsakanin $100 kan kowane gangar mai. Mun kuma gaji albashi a wannan matakin.


“Ana haka kawai sai ga wannan durkushewar sannan Najeriya ta fada cikin koma bayan tattalin arziki.”


Duk da koma bayan tattalin arzikin, ya ce mutane na sa ran ganin canji ya afku a dare daya.


“Gwamnoni ne zababbun jami’an gwamnati da aka fi zargi. Kowa na tunanin gwamnoni barayi ne kawai kuma muna banzatar da arzikin jiha, babu abunda muke yi. Ana ganin gwamnoni na jan kaya da sunan tsaro. Idan mutane suka ji kudin tsaro, suna ganin kudi ne na gwamnoni, don haka ake yi mana mugun kallo a waje.


“Alhalin, muna rike da daya daga cikin ayyuka mafi wahala a duniya. Kuma mu wani yanki ne na kasa; akwai ka’ida a wajen rancenmu. Gwamnatin tarayya na iya buga kudi. Amma mu ba za mu iya ba.


“Baya ga Lagas, yan tsirarun gwamnatocin jiha ne ke da damar yin abunda za su iya yi saboda baya ga Lagas, kowace jiha ta dogara ne da kudi da ake tura mata daga asusun tarayya. Kuma idan suka yi kasa, ka shiga matsala. “


A wani labari na daban, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba yin amfani da isarsa ba ta yadda bai dace ba.


El-Rufai ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin tsokaci a kan zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a ranar Asabar da ta gabata, The Cbale ta tabbatar.


Godwin Obaseki, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben, ya kada Ize-Iyamu na jam’iyyar APC da tazara mai yawa.


A yayin jawabinsa a shirin Sunrise Daily, wani shiri na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya ce yana fatan APC za ta ci zaben.

0 Response to "Abin Takaici Ne Yadda Jama’a Ke Mana Kallon Ɓarayi – Gwamna El Rufa’i"

Post a Comment