--
Akwai ladubba masu yawa da ake son mai azumi ya kiyaye. Ga Kaɗan daga cikin su:-

Akwai ladubba masu yawa da ake son mai azumi ya kiyaye. Ga Kaɗan daga cikin su:-


 LADUBBAN DA AKE SO MAI AZUMI YA KIYAYE SU DARASI NA 8


Akwai ladubba masu yawa da ake son mai azumi ya kiyaye. Kaɗan daga ciki su ne:


1. Yin sahur saboda hadisin Anas inda ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ku yi sahur a cikin sahur akwai albarka.” () 

Haka nan mutum zai iya yin sahur ko da da dabino ne. Saboda hadisin Abu Hurairah رضي الله عنه da ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Madalla da yin sahur ɗin mumini da ya yi da dabino.” 


Sannan kuma an so a jinkirta sahur, saboda hadisin Anas Ɗan Malik رضي الله عنه da Zaidu Ɗan Sabit رضي الله عنه suka ce, mun yi sahur tare da Manzon Allah ﷺ sannan sai ya tashi zuwa salla , sai a ka ce tsakanin gama sahur ɗinku da tayar da sallarku zai kai kimanin ya ya?” Sai suka ce, zai kai kimanin a karanta aya hamsin (50). () 

Hadisi ya zo daga Abdullahi Ɗan Umar رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana da masu kiran sallah biyu Bilalu رضي الله عنه da Abdullahi Ɗan Ummi Maktum رضي الله عنه, sai Manzon Allah ﷺ ya ce, “Shi Bilal رضي الله عنه yana kiran sallah ne da daddare, ku ci ku sha har sai kun ji Ibn Ummi Maktum رضي الله عنه ya yi kiran sallar, tsakaninsu ya zama kamar gwargwadon wannan ya sauka ne, wannan ya hau.” 


2-    Gaggauta buɗabaki, an ruwaito daga Sahlu Ɗan Sa’ad رضي الله عنه yana cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Mutane ba za su gushe ba, suna cikin alkhairi da riskar alkhairi, matuƙar suna gaggauta buɗa baki.” ()


Anas Ɗan Malik رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana fara yin buɗabaki ne, sannan sai ya zo ya yi sAllah. Ya kasance yakan ci ɗanyen dabino ko bushasshe in kuma babu sai ya kwankwaɗi ruwa kwankwaɗa.” ()


3-    Yin addu’a lokacin buɗabaki, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Umar رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya yi buɗa baki yakan ce,

((ذَهَبَ الظَّمَأُ وَابْتَلَّتِ الْعُرُوقُ وَثَبَتَ الْأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللهُ)) ()

Ma’ana: “Qishirwa ta tafi, jijiyoyi sun jiƙa, lada kuma ya tabbata da yardar Allah.”


4-    Mutum ya kiyaye gaɓɓansa ga barin abin da zai ɓata darajar azuminsa, wato ya nisanci gulma, da qarya, da cin amana, da ha'inci, da kage, da shaidar zur, da annamimanci, da duk wasu ayyukan da zasu iya jawo masa zubewar mutuncinsa a wajen Allah ﷻ. Saboda hadisin Abu Hurairah رضي الله عنه da Ma’aiki ﷺ ya ce, “Wanda duk bai daina faɗar maganar ƙarya, da aiki da ƙarya ba, Allah ﷻ ba ya da buƙatar (mutumin) ya daina cin abincinsa ko shan abin shansa.” Ma’ana, ko ya ci ko ya sha duk ɗaya ne, domin dai ba azumi yake yi ba. 

Abu Hurairah رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Da yawa mai azumi ba shi da ladan azumin nasa, sai dai ƙishirwar banza, da yawa mai sAllah ba shi da ladan sallar sai rashin barci.” ()


5-    Yawan kyauta a watan azumi, da yawan karatun Alqur’ani da yawan koyar da shi, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Abbas رضي الله عنها inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance mafi alkhairin mutane, kuma ya kasance mafi alkhairin lokacin da ya fi kowane lokaci kyauta shi ne a watan Ramadan a yayin da Mala’ika Jibrilu عليه السلام yake haɗuwa da shi, sukan haɗu a kowane dare na watan Ramadan har watan ya wuce, ya kasance Jibrilu عليه السلام yana bujuro masa da Alqur’ani suna yin bitar sa tare. Manzon Allah ﷺ shi ne mafi kyauta a kan sauran mutane, fiye da alkhairin tatacciyar iskar da aka sako.” ()


6-    Ana so mai azumi ya yawaita ibada a dare da rana a watan Ramadan, saboda hadisin Ummina Ai’shah رضي الله عنه cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance idan goman ƙarshe ya shigo yakan raya dare da ibada, kuma yakan tashi iyalansa suma su raya darensu, sannan ya kasance yakan ci ɗamara, ma’ana yakan dage sosai wajen ibada.” ()

0 Response to "Akwai ladubba masu yawa da ake son mai azumi ya kiyaye. Ga Kaɗan daga cikin su:-"

Post a Comment