--
BREAKING NEWS:- Mun Kori Sheikh Nuru Khalid daga limanci Gaba Daya Tunda baiyi Nadama ba- Sanata dan Sadau

BREAKING NEWS:- Mun Kori Sheikh Nuru Khalid daga limanci Gaba Daya Tunda baiyi Nadama ba- Sanata dan Sadau


 Shugaban kwamitin Masallacin APO dake Abuja Sanata Dansadau ya sanar da korar limamin masallacin wanda aka dakatar a karshen makon jiya.


A takardar korar wanda kwamitin masallacin APO ta aika wa liman Sheikh Nuru Khalid, bai nuna nadamar kalaman da yayi da suka yi sanadiyyar aka dakatar dashi daga limancin masallacin.

” Kwamitin masallaci ta sallami sheikh Nuru Khalid kwata-kwata daga limancin masallacin APO daga yau litin 4 ga wata. Haka take a takardar wacce shugaban kwamitin Sanata Dansadau ya saka wa hannu.

Ƴan Najeriya da dama sun nuna rashin jin daɗin su da dakatar da limamin masallacin Apo dake Abuja Sheikh Nuru Khalid

Idan ba a manta ba kwamitin masallacin Juma’a na APO dake Abuja sun dakatar da limamin saboda ya wai ya fadi wasu kalamai da za du iya ingiza matasa a samu tashin hankali a kasar nan.

Sai dai kuma kalaman wanda PREMIUM TIMES ta saurara yana gargaɗi ga gwamnatin Buhari da ta samar wa ƴan Najeriya tsaro kamar yadda ta yi alƙawari.

A cikin hudubar sa ta ranar Juma’a, Sheikh Khalid ya ce “Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,” in ji Sheikh Nuru Khalid a huɗubarsa. 

Sannan ya yi kira ga shugaba Buhari ya farfaɗo daga barcin da yake yi ya cika alkawarin samar wa ƴan Najeriya da tsaro kamar yadda yayi a baya.

” Tsakani da Allah ku duba ku ga yadda ake kashe mutane kamar kaji, ni idan ba za a gaya wa Bugari gaskiya ba, zan gaya masa, kasa fa ta na cikin matsala na rashin tsaro matuka.

” Ya kai ga an wayi gari a Najeriya ƴan bindiga na karɓar haraji a ƙasar nan. Wanda doka gwamnati kawai ta ke da wannan dama na karbar haraji amma ƴan bindiga na yi wa mutane a garuruwa da dama a kasar nan.

Sai dai kuma Sanata Saidu Dansadau wanda shine shugaban kwamitin masallacin ya ce ba tun yanzu ba mun jan wa liman Khalid kunne ya daina zafin gwamnati ya ki ji.

A martanin da ya baiwa kwamitin masallacin sheikh Khalid ya ce da a hana shi fadin gaskiya da faɗi wa gwamnati ana kashe mutane, gara ya hakura da limancin ya koma yin dako.

” Wai ace mutumin Ɗansadau Jihar Zamfara ne wanda ƴan bindiga suka yi wa garin ragaraga shine zai dakatar dani don na fadi cewa ana kashe mutane a kasar nan kuma gwamnati bata yin komai a kai. 

0 Response to "BREAKING NEWS:- Mun Kori Sheikh Nuru Khalid daga limanci Gaba Daya Tunda baiyi Nadama ba- Sanata dan Sadau"

Post a Comment