--
Jaruma Nafisa Abdullah tace a daina haifa yayan da ba za a iya kula dasu ba

Jaruma Nafisa Abdullah tace a daina haifa yayan da ba za a iya kula dasu ba




Fitacciyar Jarumar Fina-Finan Kannywood, wato Nafisa Abdullah ta Yi kira ga ‘yan Nijeriya dasu daina haifar yayan da basu iya kula dasu ba.

Ku daina haihuwar ƴaƴan da ba za ku iya kula da su ba - Inji Jaruma Nafisa Abdullahi.

Ta kara da cewa Allah zai tuhumi mutanen da suke haifar ƴaƴa ba tare da sauke nauyin da ya ɗora musu ba.


A cewarta: "Kun ga dukkan mutanen da ke haifar ƴaƴan da ba su ji ba, ba su gani ba domin kawai su aika da su almajiranci, kuma su ci gaba da haifar karin ƴaƴa, Allah sai ya saka wa yaran nan. 


Ta bayyana matukar bacin ranta kan yadda wasu iyayen suke tura ƴaƴansu ƴan shekara biyu zuwa uku almajirci.


Me za ku ce ?

0 Response to "Jaruma Nafisa Abdullah tace a daina haifa yayan da ba za a iya kula dasu ba"

Post a Comment