--
Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka

Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka


 Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka


Jaruma Nafisa Abdullahi ta yi martani mai zafi ga Sarkin Waka kan wallafar da yayi na kare iyayen da ke haihuwar yara su barsu suna almajiranci



Jarumar ta kira Naziru Sarkin Waka da mai neman suna, ta kara da cewa ta san matsalarsa kuma idan ya isa, ya bugi kirji ya kira suna ne


A cikin makon nan ne Nafisa ta caccaki iyaye da ke haihuwar yara babu kulawa suna sakinsu a titi inda suke zama almajirai


Jaruma Nafisa Abdullahi ta yi martani ga fitaccen mawaki, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Wakar San Kano.


A jiya ne mawakin yayi wata wallafa wacce kai tsaye wadanda ke bibiyar shafin jaruma Nafisa Abdullahi za su gane cewa martani ne yayi ga wata wallafar da tayi.


Jarumar ta caccaki iyayen da ke haihuwa tare da kin daukar dawainiyar 'ya'yan kuma su sake su a kan titi suna almajiranci babu tarbiya.


Babu shakka wannan wallafa ta tada kura inda 'yan Najeriya ballantana arewaci aka yi caa a kanta.



Kwatsam sai ga wallafar Sarkin Waka inda yake bayyana cewa ba almajirai bane yaran da iyayensu suka haifa suka kasa kula da su ba, idan kana son ganin 'ya'yan da iyayensu suka haifa kuma suka kasa kula dasu, toh ka taho masana'antar fim.


Jaruma Nafisa Abdullahi bata yi kasa a guiwa ba taje shafinta na Twitter inda ta yi wa mawakin martani inda ta kira shi da mai neman suna. Idan kuma ya isa, ya bugi kirji ya kira suna.


Ga martanin nata:



0 Response to "Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka"

Post a Comment