--
Yanzu-yanzu: Masu Umrah 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

Yanzu-yanzu: Masu Umrah 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

 Yanzu-yanzu: Masu Umrah 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

Labari da duminsa daga kungiyar Red Crescent a kasar Saudiyya na nuna cewa mota dauke da maniyyata masu ziyarar Masallacin Annabi (SAW) dake Madina sun samu hadari.

Haramain Sharifain ya ruwaito cewa motar mai dauke da mutum 51 ta yi juyi kan babban titi kuma mutane da dama sun jikkata.

Kawo yanzu da muke kawo rahoto an yi rashin rayuka takwas.

"Wata motar Bas dauke da masu ziyara da maniyyata 51 ta kife a titin Hijra a Madinah Al Munawarrah yau kuma mutane da dama sun jikkata, 8 sun mutu."

0 Response to "Yanzu-yanzu: Masu Umrah 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama"

Post a Comment