--
Zan kashe mutum 900 idan ba a biyani diyyar matata da aka kashe ba, Inji Dan ta'adda

Zan kashe mutum 900 idan ba a biyani diyyar matata da aka kashe ba, Inji Dan ta'adda


 


Na Bayar Da Wa’adin Mako 2 A biya Ni Diyyar Matata Ko Na Kashe Mutum 900 - Inji Ɗan Ta'addan daji A Jihar Zamfara


Wani jagoran ƴan ta'adda ya ba wa gwamnati Wa’adin mako biyu a biya shi diyyar matarsa da ‘yan uwanta Naira Miliyan 30, ko ya kashe mutane 900 a Zamfara.


Ɗan Ta'addan da akafi sani da Nasanda, wanda yayi sansanin a dajin Dumburu na jihar, yayi barazanar Kashe Mutum 300 a duk rai daya na ‘yan uwan matarsa da ya ce wai an kashe. Tare da cewa ya kwashe sam da shekaru 4 yana kisan bayin Allah a wadannan yankuna. Yan daya daga cikin wadanda aka yi sulhu da su a baya kafin ya sake komawa daji ya ci gaba da saya da kisa.


Ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan murya da Jaridar HumAngle ta fitar, ya bayyana yadda ‘yan Sa-kai da gwamnatin jihar suka kashe sabuwar amaryarsa, da kawunta, da kuma kanwarta, bisa laifin zarginsu da hada baki da ‘yan ta’adda a yankin.


“Ba wa’adin watanni zan bayar ba, zan bada kwanaki 14 don biyana diyya. Kuma ba za mu kai hari ba har sai sun shirya yin noma; za mu yi zango a cikin al’ummominsu.


“Idan an bar Fulani su zauna lafiya, mu ma za mu bar kowa cikin kwanciyar hankali. Idan gwamnati ba za ta iya biyan kudin ba, zan yi abin da na saba yi.” inji shi.

0 Response to "Zan kashe mutum 900 idan ba a biyani diyyar matata da aka kashe ba, Inji Dan ta'adda"

Post a Comment