SUBHANALLAH: Faɗa ya ɓarke a Masallacin Ka’aba na Saudiyya
Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun tabbatar da cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne wani rikici ya barke tsakanin wasu mutane guda biyu, a gaban Masallacin Harami da ke kasar Saudiyya.
Tuni dai jami’an tsaron kasar suka tsananta bincike game da wannan lamarin.
Majiyar jaridar Arewa ta samo labarin daga Saudi Gazzety wanda suka tabbatar da faruwar lamarin, Amma ance ba a samu wanda ya samu rauni ba daga cikin mutane biyun da suka yi fadan. Sai dai Hukumomin tsaro sunce zasu gaggauta daukar mataki a kansu.
0 Response to "SUBHANALLAH: Faɗa ya ɓarke a Masallacin Ka’aba na Saudiyya"
Post a Comment