--
Da Ziyarar Kabarin Shehu Danfodio Da Ziyarar Kabarin Kafiri Clapperto Duk Daya Ne ~ Sheikh Musa Ayuba Lukuwa

Babban malamin addinin musulunci a jihar Sokoto Sheikh Musa Ayuba ya yi kira ga gwamnatin jihar Sokoto da fadar sarkin musulmi da su gaggauta haramta ziyarar da ake kawo wa ga kabarin babban Malamin addinin musulunci na Africa Sheikh Usmanu Fodio daga sassa daban-daban ciki da wajen Najeriya.

Malamin yace ana ziyarar kabari ne saboda tunawa da mutuwa, don haka masu kawo wannan ziyara su tsaya a garuruwan su domin a can ma akwai kaburbura wadanda zasu ziyarta su tuna da mutuwa.

Malamin ya ce wannan ziyara da wadanna Fulani su ke kawo wa a Hubbaren Shehu Danfodio ta sa6awa addinin musulunci, don haka akwai bukatar a haramta wannan ziyara.

Malamin ya ci gaba da cewa "Kamar yadda kasan idan ka ziyarci kabarin kafiri Clapperto bakada lada haka ma ziyartar kabarin Danfodio babu mai baka lada". 

Hakama, Malamin ya ce kai ko kabarin Annabi ka tashi daga Sokoto ka je Madina domin ziyara bakada lada ko guda.

~ Nasara

0 Response to "Da Ziyarar Kabarin Shehu Danfodio Da Ziyarar Kabarin Kafiri Clapperto Duk Daya Ne ~ Sheikh Musa Ayuba Lukuwa"

Post a Comment