--
Kuskure Biyar Da Samari Suke Yi A Yayin Da Suke Neman Aure

Kuskure Biyar Da Samari Suke Yi A Yayin Da Suke Neman Aure


Aure wani ginshiƙi ne na jin daɗin rayuwar duniya, sannan kuma abu ne da kowa ke burin ya yi a rayuwarsa kodai namiji ko mace. Bugu da ƙari kuma, aure yakan ƙarawa masu yinsa ƙima da daraja a idanun duniya.


Amma kuma yin auren ba shine abu mafi muhimmanci ba, samun mallakar abokin zama na gari shine babban abinda ake buƙata a rayuwar aure. Kuma akan samu zaman lafiya ne a gidan aure idan har aka shimfiɗa soyayya a kan tubalin gaskiya, yarda da kuma amana.


Mazaje da dama sukan yi kuskure wajen neman matan aure. Don haka mukayi amfani da wannan dama wajen zayyano muku wasu daga cikin manyan kura-kurai da maza suke yi a wajen neman aurensu, domin su gyara ko don auren su ya ɗore.


Ga dai kaɗan daga cikin irin waɗannan kura-kuren da maza suke aikatawa kamar haka:


1. Ƙarya: 


Ƙarya tana daga cikin irin abubuwan da ke zubar da mutuncin mutum wajen wacce zai aura. sai kaga matashi yana zuwa wajen budurwa amma yana yi mata ƙarya kuma wai aurenta zaiyi, kaji yana cewa ai shi mai arziki ne, idan ta aure shi ta huta. Ya riƙa karɓar aron abubuwan duniya don ya ruɗe ta dasu ko kuma ya birge ta. Wannan shi ne mataki na ƙarshe a rashin wayewa, da fatan samari masu irin wannan halin za su faɗaka su daina.


2. Rowa: 


Rowa na ɗaya daga cikin irin kuskuren da samari suke aikatawa a wajen ƴan matan da zasu aura. Dukkan mace tana son kyauta, ya zamana hannun saurayi a buɗe yake. Duk da ba a ɗaura sharaɗin aure kan yin kyautar kuɗi ba, amma Manzon Allah (saw) ya faɗi cewa, “Zuciya tana jawuwa bisa son wanda yake kyautata mata, sannan tana ƙin wanda ya munana mata”. Kenan ashe kyauta za ta iya taka muhimmiyar rawa a wajen neman aure. Wasu samarin nada tunanin cewa tunda ba aure suka yi ba, bazasu riƙa bada kyauta ba.


3. Rashin neman mai kyaun dabi’a: 


Babban kuskuren da samari suke aikatawa a wannan zamanin shine rashin tunkarar mace mai tarbiyya ilimi da kyan ɗabiu, su aninda suke dubawa kyau da ƙyale-ƙyali. Abin da ya kamata ka fi mayar da hankali a kai shi ne, neman mace mai kyawawan dabi’u, wacce za ka iya zama da ita don Allah, wacce za ta kai ka tudun-mun-tsira, ba wacce za ta kama hannunka ku tsunduma cikin wuta ba, Allah ya kare.


4. Kazanta(rashin tsafta): 


Tana daga cikin abubuwan dake jawo mutum ya rasa ƙima a wajen mace saboda gaskiya mata na da tsabta yadda ya kamata, saboda haka ba sa son namiji ƙazami. Abin alfaharin Mace ne ta nuna ka a gaban ƙawayenta ka yi wanka mai kyau, ka haɗu. Amma su wasu samarin babu ruwan su sai kaga mutum babu kwalliya babu gyara jiki. Don haka yana da kyau masu irin wannan halin su gyara.


5. Ƙarancin wayewa: 


Yawancin lokaci wasu mazan sukan yin gaba da mace, sai su riƙa nuna tsanin wayewarsu ta zamani. A ganinsu wannan ne dalilin da zai sa su karɓu wajen mace. Sannan a hakan kuma saboda rashin wayewar tasu, babu abin da za su fi mayar da hankali a kai illah neman wacce wai take da wayewar Zamani. Wannan ba ɗabia ce mai kyau ba.


Wannan sune kaɗan daga cikin jerin irin kuskuren da maza suke aikatawa a yayin neman auren su. Abubuwan suna da yawa amma ba za mu iya kawo muku su a wannan lokacin ba, sai dai anan gaba Insha Allah za kuji mu da ƙarin wasu. Da fatan samari idan an tashi neman aure za'a kiyaye da waɗannan abubuwan da muka ambata a sama. Allah yasa mu dace amin.

0 Response to "Kuskure Biyar Da Samari Suke Yi A Yayin Da Suke Neman Aure"

Post a Comment