--
Yadda Zulum Ya Sa A Zane Wani Talaka Don Ya Bi Layi Zai Karbi Tallafin Da Za A Raba

Yadda Zulum Ya Sa A Zane Wani Talaka Don Ya Bi Layi Zai Karbi Tallafin Da Za A Raba


 Yadda Zulum Ya Sa A Zane Wani Talaka Don Ya Bi Layi Zai Karbi Tallafin Da Za A Raba


...an yi kira ga kungiyar yancin dan Adam ta hukunta Zulum kan cin zarafin wannan matashi


Daga Muryoyi 


Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya sa a zane wani matashi saboda ya bi layin karban tallafi da Gwamnan zai rabar


Muryoyi ta ruwaito an ga yadda Gwamnan ya tsawatawa matashin cewa ya tashi ya fita sannan yasa ayi masa bulala da duk matasan da suka shiga layin wadanda za ayiwa rabon tallafin. 



Wannan lamari bai yiwa wasu dadi ba inda suke cewa anci zalin matashin wasu kuma na cewa ya kamata yan kungiyar kare yancin dan Adam su tuhumi Gwamnan kan yadda zai tozarta matashin don kawai zai karbi hakkinsa "ai kayan na Gwamnati ne kuma shima matashin dan kasa ne" to menene na sakawa a dake shi? Wasu kuma na cewa Boyayyen mugun halin Zulum din ne ya soma fitowa fili tunda yana nunawa talakawa kyara sai dai wasu sun nuna nasu mabanbantan ra'ayin 


Me za ku ce?

0 Response to "Yadda Zulum Ya Sa A Zane Wani Talaka Don Ya Bi Layi Zai Karbi Tallafin Da Za A Raba"

Post a Comment