--
Yadda Zaka Samu OTP Na manhajar Nimc Ko Da Layinka Ya Bata Yayin Bude App

Yadda Zaka Samu OTP Na manhajar Nimc Ko Da Layinka Ya Bata Yayin Bude App


Kasancewar wasu suna da bukatar login domin printing ko ganin bayanan NIMC naka Amma baka da damar yin hakan domin Karasa Number wayar ka


Insha Allah idan kabi wannan hanya zaka samu damar yin login na NIMC APP dinka acikin sauki


Dafarko kashiga A play store kayi download na NIMC APP


Bayan ka dakko shi, sai ka bude ka sanya lambar NIN din da kake son ganin bayanan ta, daga nan za su tura OTP a lambar da aka bude NIN din da ita,


Idan baka da lambar da aka tura OTP din cikin ta, sai ka samu layi mafi kusa da kai ka danna *346*2*NIN# Ka danna alamar kira📞 misali *346*2*22334455667# (za ka sanya lambar NIN din da ka sanya a cikin application din ne)


Ka tabbatar akwai katin ₦20 ko fiye da haka a layin da ka danna lambobin! Idan kayi komai daidai to nan take zaka ga User ID da OTP na wannan NIN din sun bayyana, sai kayi amfani da OTP din a cikin Application din

Kana sanya wa zai wuce, zai kai ka inda za ka sa password 🔑 sai ka zaɓi lambobi guda shida ka sa, ka sake maimaita su, shikenan zai wuce successfully ✅


ABIN LURA

Dole sai kayi requesting OTP ta cikin Application din, sannan ka danna lambobin, sannan kuma ka tabbatar baka dauki dogon lokaci tsakanin requesting na OTP din da danna lambobin ba, domin yin hakan zai iya baka matsala


✍️✍️

FUTURETECH GUID


Hkk Weblearner

0 Response to "Yadda Zaka Samu OTP Na manhajar Nimc Ko Da Layinka Ya Bata Yayin Bude App"

Post a Comment